mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

KAFIN ANNABI YA SANAR DA ALI KOFOFIN ILIMI SHIN ALI YA JAHILCE SU

Salamu Alaikum wani daga cikin mabiya mazhabar sunna ya tambaye ni ya ce: ashe Imam Ali bai fadi cewa Annabi (s.a.w) ya sanar da shi kofofin ilimi ba kuma kowacce kofa tana bude masa kofofi dubu, tambaya anan shi ne kafin Annabi ya sanar da shi wadannan kofofi shin ya kasance yana jahiltarsu? Ina fatan samun amsa a take na gode

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Imam bai jahilci wadannan kofofi a duniyoyin da suka kasance gabanin wannan duniya ta gangar jiki duniyar da muke cikinta lallai iliminsa daga ilimin Annabi yake kuma ilimin Annabi daga ilimin Allah yake cikin dukkanin duniyoyi cikin Kausul nuzuli da su’udi, sai dia cewa cikin duniya kamar yanda ta kasance gidan neman sani da neman ilimi da koyo to ya zama dole a bayyanar da wadancan ilimummuka da suka kasance gabani, sabida haka ne ma yake cewa Manzon Allah (s.a.w) ya sanar dani kofofi dubu daga ilimi daga kowacce kofa kofa dubu tana budewa ma’ana kofa miliyan daya, hakika babban malami masanin ilimin falsafa mutumin birnin Mashada ya wallafa littafi mai suna milyoyin ilimummukan zamani asalin su daga Sarkin Muminai (a.s) suke ina da wannan littafi daya cikin mujalladi goma,

Wurin ubangiji muke neman taimako.
Tarihi: [2019/12/4]     Ziyara: [491]

Tura tambaya