mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Zantukanku haske



Ladubban karatun kur'ani

رسول الله (ص):

«نَوِّرُوا بُيُوْتَكُمْ بِتَلاوَةِ الْقُرْآنِ وَلا تَتَّخِذُوها قُبُوْراً كَما فَعَلَتِ اليَهُوْدُ والنَّصارى، صَلّوا في الكَنائِس وَالْبِيَع وَعَطَّلُوا بُيُوْتَهُم، فَإِنَّ الْبَيْتَ إِذا كَثُر فيهِ تِلاوَةُ الْقُرآنِ كَثُرَ خَيْرُهُ واتَّسَعَ أَهْلُه وَأَضاءَ لأَهْلِ السَّماءِ كَما تُضِيْ‏ءُ نُجُوْمُ السَّماءِ لأَهْلِ الدُّنْيا.

(أصول الكافي ج 4 ص 413)


Ladubban karatun kur'ani

رسول الله (ص):

«نَوِّرُوا بُيُوْتَكُمْ بِتَلاوَةِ الْقُرْآنِ وَلا تَتَّخِذُوها قُبُوْراً كَما فَعَلَتِ اليَهُوْدُ والنَّصارى، صَلّوا في الكَنائِس وَالْبِيَع وَعَطَّلُوا بُيُوْتَهُم، فَإِنَّ الْبَيْتَ إِذا كَثُر فيهِ تِلاوَةُ الْقُرآنِ كَثُرَ خَيْرُهُ واتَّسَعَ أَهْلُه وَأَضاءَ لأَهْلِ السَّماءِ كَما تُضِيْ‏ءُ نُجُوْمُ السَّماءِ لأَهْلِ الدُّنْيا.

(أصول الكافي ج 4 ص 413)

Manzon Allah (s.a.w) yace: ku haskaka gidajenku da tilawar kur'ani ka da ku maida gidajenku kaburbura kamar yanda Yahudawa da Nasara suka aikata, suna ibadunsu cikin majami'u da coci-coci suka wofintar da gidajensu daga ibada, lallai shi gida idan aka yawaita tilawar kur'ani cikinsa sai alherinsa ya yawaita ahalin gidan su samu yalwa ya haskaka halittun sama kamar yanda taurari suke haskaka halittun kasa.

الرسول الأكرم (ص):

«عن النبي (ص) أنَّهُ سُئِلَ أَيُّ النَّاسِ أَحْسَنُ صوتاً بِالقُرآنِ؟ قالَ مَنْ إذا سَمِعْتَ قِراءَتَهُ رَأَيْتَ أَنَّهُ يَخْشَى الله».

(البحار ج 89 ص 195)

Manzo mafi karamci (s.a.w): wata rana an tambaye shi wanne mutum yafi kowa kyawun sauti? Sai yace: shine wanda idan kaji karatunsa sai ka gan shi yana tsoran Allah.

الإمام الصادق (عليه السلام):

«مَنْ اسْتَمَعَ حَرْفاً مِنْ كِتابِ اللهِ مِنْ غَيْر قراءَة كُتِبَ لَهُ حَسَنَةٌ وَمُحِيَ عَنْهُ سَيِّئَةٌ وَرُفِعَ لَهُ دَرَجَةٌ».

(عدة الداعي ص 211)

Imam Sadik (as) duk wanda ya ji harafi daya daga littafin Allah ba tareda karatu ba za a rubuta masa kyakkyawan aiki guda a shafe masa zunubi guda sannan a daukaka darajarsa.

رسول الله (ص):

«اقرأوا القُرآنَ بِألْحانِ العَرَبِ وأصْواتِها».

(الكافي ج 4 ص 419)

Manzon Allah (s.a.w): ku karanta kur'ani da Karin muryar larabawa da sautinsu.

الإمام الصادق (عليه السلام):

«... كانَ أصْحابُ مُحَمَّد (ص) يَقْرأ أَحَدُهُمْ الْقُرآنِ في شَهر أَوْ أقَلَّ إنَّ الْقُرآن لا يُقْرأُ هَذْرَمَةً وَلكنْ يُرَتَّلُ تَرْتِيلًا فَإِذا مَرَرْتَ بِآيَةٍ فِيها ذِكْرُ الْجَنَّة فَقِفْ عِنْدَها وَسَل الله عزَّ وَجَلَّ الْجَنَّةَ وإِذا مَرَرْت بِآيةٍ فيها ذِكْرُ النَّار فَقِفْ عِنْدَها وَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنَ النَّارِ».

(أصول الكافي ج 4 ص 422)

Imam Sadik (as): sahabban manzon Allah (s.a.w) sun kasance dayansu yana karance kur'ani cikin watan Ramadan ko kasa da wata, lallai shi kur'ani….. sai dai cewa ana jeranta shi jerantawa, idan ka gifta da wata aya wacce cikin aka ambaci aljanna to ka tsaya wurinta ka roki Allah aljanna, idan ka gifta da wata aya da aka ambaci wuta cikinta ka tsaya ka nemi tsarin Allah daga wuta.

الإمام الصادق (عليه السلام):

«ما يَمْنَعُ التَّاجِرُ مِنْكُم، المَشْغُولُ في سُوقِهِ إذا رَجَعَ إلى مَنْزِلِهِ أَنْ لا يَنَامَ حَتَّى يَقْرأ سُوْرَةً مِنَ الْقُرآنِ فَتُكْتَبُ لَهُ مَكانَ كلِّ آيةٍ يقْرؤُها عَشرُ حَسَناتٍ ويُمْحى عَنْهُ عَشْرُ سَيِّئاتٍ».

(أصول الكافي ج 4 ص 414)

Imam Sadik (as): mene ne ya hana attajirin cikinku wanda ya shagaltu da kasuwarsa idan ya dawo gida daga kasuwa kafin ya kwanta barci ya karanta wata sura daya daga kur'ani sai a rubuta masa ladan aiki goma kan kowacce a kuma kankare masa zunubi goma.

Tarihi: [2019/3/14]     Ziyara: [546]

Tura tambaya