sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Watsa muhadarar Samahatus Sayyid Adil-Alawi kai tsaye a tashar Assaklain
- Labarai » • Samahatus Sayyid Adil-Alawi zai gabatar da muhadara cikin Haramin Sayyida Ma'asuma a ranar mauludin Sayyada Fatima (as)
- Labarai » Sirrin dawwama wani shiri ne daga Assayid Adil-Alawi da yake gudana cikin watan Muharram
- Labarai » Majalisin ta’aziyya da zaman makokin shahadar sayyada Fatima zahara (as) tareda halartar shaik muntazar wa’izi da fadilatul Sayyid Adil-Alawi (h) da kuma mawakin Ahlil-baiti Husaini Ammar kinani
- Labarai » Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
- munasabobi » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
- Labarai » Sayyid adil alawi ya dawo daga tafiyarsa ta tabligi
- Labarai » Raya daren lailatul qadr tare da sayyid adil alawi
- munasabobi » Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
- Labarai » Darasi da ga rayuwar imam jawad
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » MUHADARAR SAYYID ADIL ALAWI 1438 HIJRA KAMARIYA
- Labarai » Ubangiji ya girmama ladanku da namu bisa wafatin Sayyada Zainab diyar Imam Ali bn Abu dalib (as)
- Labarai » Bikin murnar zagayowar Ranar Auren haske biyu
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
(اللّهم إني أسألك من نورك بأنوره وكلّ نورك نيّر اللّهم إني أسألك من نورك كلّه)
Ya Allah lallai ni ina rokonka daga haskenka da dukkanin haskenka mai haskaka ya Allah ina rokonka daga dukkanin haskenka.
Babu shakka lallai manzon Allah (s.a.w) ya na da wannan siffa haka ma imami (as) bayansa sasanni uku: sasannin mutumtaka da sasannin annabtaka da imamanci a sasannin wilaya.
Amma na farko: lallai babu banbanci tsakaninsu da kowanne mutum daga mutane kamar yadda madaukaki ya ba da labar:
﴿قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ﴾(فصلت: 6
Kadai dai ni mutum ne irinku.
Ya na ci ya na sha ya na yin rashin lafiya ya na warkewa ya na jin yunwa koshi ya na jin kishurwa ya na koshi da dai wasunsu daga ayyukan da dukkanin dan adam ke gogayya da su.
Lallai kamar ydda ake cewa cikin ta’arifin mutum cikin ilimin mandik da cewa shi mutum shi ne : (dabba mai magana) lallai annabi mafi girma misdakin ne daga misdakan mutum, amma kamaloli na nafsu na zati da masu bijirowa basu yin tasiri cikin wannan mafhumi na mandik, lallai ana amfani da kalmar mutum kan jahili da mai ilimi da talaka da mawadaci haka dai, gasgatuwarsa kadai dai ya na daga bangaren mahiyyar mutum kawai, idan ba haka sauda yawa za a iya samun banbanci tsakanin misdaki da misdaki ta fuskanin huwiyya mutumtakarsu (hakinani) da hali na zati wanda zai iya kaiwa banbanci nisa tsakanin sama da kasa, yaushe za a hada salihi da azzalumi da yau she alheri sharri zamuzamo abu guda, yau she za a hada tsaftatacce da mai kazanta, ina mumini ina kafiri, daga cikin mutane akwai wanda shi na sama ne da malukutiyya cikin halayensa, sannan daga cikinsu kuma akwai wanda kasa ya ke ya kuma kasance kasan kaskantattu. Sannan mutum bil adama kamar ragowar dabbobi ne ya na kasantuwa daga maniyyi daga sinadarai sanannu cikin tsatson mazaje sannan ya dawo ya tsuguna a mahaifa ya dinga kammaluwa a hankali a hankali har yakai ga marhalar haifarsa mutum yaro karami sannan ya dinga tsallake marhaloli rayuwarsa daga yarinta da bauta da samartaka da tsufa gazawa daga karshe kuma ya karkare ga mutuwa
﴿كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ﴾ (آل عمران: 185)
Dukkanin mai dandanar mutuwa ce.
﴿إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُمْ مَيِّتُونَ﴾ (الزمر: 30)،
Lallai kai mai mutuwa ne lallai su ma zasu mutu.
Wannan cikin janibin kasantuwa mutum kenan lallai shi an tilasa shi kan tsarin dabi’ar halittarsa ta fuskanin samuwarsa ta gangar jiki, duk da kasantuwa dabi’a an buwayar da ita ga annabi da imami ta janibin wilaya, misalinsa kamar wanda ya ke kera jirgin zuwa sararin samaniya, lallai lokacin hawansa cikinsa zuwa sararin samaniya, babu banbanci cikin taklifinsa da na waninsa daga kiyaye dokoki da sharuddan hawa da sauka, kamar wanda ya hau tauraro, lallai shi an hukunta shi da dabi’arsa ta mutum da garizarsa da tsarin halittarsa da dabi’unsa.
Na’am kadai dai annabi da imami suna banbanta da sauran mutane cikin tsarkakar asalin da suka fito daga cikinsa da tsarkin haihuwarsa cikin tsarkakakken tsatso da tsarkakkiyar mahaifa kamar yadda muke karantawa cikin ziyararsu
(أشهد إنك الطاهر المطهر كنت في الأصلاب الطاهرة والأرحام المطهرة)
Ina shaidawa lallai kai tsarkakakke ne ka kasance cikin tsatso tsarkakake da mahaifu tsarkakakku.
Amma ragowar siffofi mutum kamar misalin launi da shakali da tsarin dabi’a annabi da imami basu da banbanci da sauran mutane, ta yiwu su zama farare ta yiwu su kasance launin wankan tarwada wanda kalarsa tafi karkata zuwa ga launi baki kamar misalin imam jawad (as) ta yiwu ya zama rarrauna ramamme ta yiwu kuma ya zama mai kiba da girman jiki kamar misalin imam bakir (as) wadannan siffofi da halaye basu da wani tasiri cikin sakonsu da imamancinsu da wilyarsu, lallai shi annabi ko imami wannan abubuwa basa fitar da shi daga kasantuwarsa mutum bil adama da abin da yan adamtaka ke hukuntawa.
Na biyu: annabta da imamanci; lallai kalmar annabi a asali daga annabwatu take wacce take da ma’anar daukaka ko kuma daga Kalmar naba’u wacce take dda ma’anar labari nabiyu wanda ya ke zuwa da labaran sama da wahayi daga Allah matsakaki cikin bayanin hukunce-hukuncen shari’a da addini domin shiryar da mutane da farin cikinsu da kamalarsu.
Imama: hakika ya zo cikin ta’arifinta cikin ilimin kalam da cewa: ita shugabanci ne mai gamewa cikin duniya da lahira wakilantaka daga manzon Allah (s.a.w) a wajen yan imamiya isna ashariyya: da nassin daga Allah matsarkaki da nasabtawa daga manzonsa, amma wajen wadanda bay an imamiya ba imamanci na kasancewa da shura da zabin mutane, imamanci a sakafar isdilahin shi’a tana shiryarwa kan cewa hukumar imami ma’asumi kamar hukumar annabi ce kan mutane ba tare da wani banbanci ba, wajibi ne ai masa biyya kamar yadda ya wajaba ayiwa Allah biyayya da manzonsa.
﴿أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُوْلِي الأَمْرِ مِنْكُمْ﴾ (النساء: 59)،
Ku bi Allah ku bi manzon Allah da ma’abota al’amari daga gare ku.
Kadai dai biyayya mudlaka ga imami tana wajabta ne sakamakon ismarsa kulliya ta zati sakamakon iliminsa daga Allah da wilayarsa mafi girma, da la’akari da wannan matsayi na Allah da annabi ya zamanto daga hakkinsa tsayar da hukuma da daula da alkalanci da zartar da haddodi dsa tsayar sallar juma’a da sulhu da yaki da wasun haka daga batutuwa na siyasa da al’amuran da suka shafi tattalin arziki da batutuwan zamantakewa da sakafa da makamantansu, banbanci tsakanin annabi da imami wasiyyi da sauran mutane shi ne cewa cikin annabi shi ne akwai wahayin Allah
﴿قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ يُوحَى إِلَيَّ ﴾ (الكهف: 110)،
Ka ce kadai dai ni mmutum misalinku ana wahayi zuwa gare ni.
Cikin imami shi ne akwai isar da sakon shari’a da kiyaye abin da annabi ya zo da shi da zartar da sakon saukakakke, lallai shi imami ya na matsayin majalisin zartarwa ne kamar yadda shi kuma annabi ke bayyanuwa cikin matsayin majalisar dokoki.
Dukkanin wadannan mukaman Allah da kamalolin zati kadai dai suna bubbuga da fitowa daga wilayarsu mai girma, hakika wilayar imaman tsira da shiriya cikin tsahon wilayar annabi mafi girma, ita kuma wilyar annabi ta cikin tsahon wilayar Allah matsarkaki
﴿هُنَالِكَ الْوَلايَةُ لِلَّهِ الْحَقِّ﴾ (الكهف: 44)،
A can jibanta ga Allah ya ke shi ne gaskiya.
Wilyar Allah a asali kuma cikin mukamin wajibin samuwa ga zatinsa, da wilayar waliyyansa da bi cikin mukami imkanin zati, cikin nufar dukkanin bukatuwa zuwa ga Allah da wadauwarsa, ita wilayar imamai tsarkaka ana kiranta da sunan wilaya kamariya, ita kuma wilayar annabi mafi girma ana kiranta da wilaya shamsiya. Banbanci tsakaninsu a bayyane ya ke lallai shi hasken wata daga hasken rana ya ke, sannan shi kuma hasken rana daga hasken ubangijinta ya ke
﴿وَأَشْرَقَتْ الأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا﴾ (الزمر: 69).
Sai kasa ta haskaka da hasken ubangijinta.
Cikin annata da imamanci annabi da imami suna fifita kan ragowar mutane da ma’asumancinsu na zati da iliminsu daga Allah, da kuma kasantuwarsu mafi kamala mutanen zamaninsu cikin kayawawan halaye da falaloli da kamaloli. Sannan bayan wadannan mukamai biyu annabta da imamanci lallai su hujjojin Allah ne kan dukkanin halittu baki daya, lallai ga imami da ma’anarsa mai gamewa wacce take tattaro annabi da wasiyyi da mukamin hujja, lallai Allah ya na kafa hujja da shi kan halittu kamar yadda halittu suke kafa hujja da shi, wannan ya na daga imamancinsa na halitta ballantana imamancinsa na shari’a da imamancinsa na duniya, saboda haka imamancinsu ba ta tsaya iya kan mutane da bil adama ba kadai ba bari dai ta mamaye ta game dukkanin halittu da samammu madaukaka da makaskanta cikin dabi’a da abin da ya buyar ma dabi’a, shi mulkar mutane kadai dai shi ya na daga sasannin gamammiyar imamanci.
Daga bayya nanne al’amari shi ne lallai mulkinsu kan mutane kadai daukaka ce da imamancinsu ba sabani haka ba, mune wadanda zamu yi alfahari da su imamanmu ma’asumai masu shiryarwa madamaita (as) bawai sune masau alfahari da maulkarmu ba da hukumarsu ta zahiri da badini kanmu, shugabancin duniya bai yin wani tasiri cikin wilayarsu mai girma ta Allah mai zartuwa cikin halitta da shari’a, hukuma wacce take da ma’anar gamamman jagoranci na zahiri kadai ita cikin duniya take tana kuma ratayuwa da batutuwanta zai ma ikya yiwuwa imami bai jibance ta ba kai tsaye take, ta yiwu wasu al’amurra su hukunta cewa ya nesanta kansa daga gareta wani lokaci, kamar yadda ya kasance ga mafi yawan imamanmu musammam ma idan mutane sukai watsi da rungumarsu da zuwa inda suke, sai dai cewa hukuma ta boye ta badini kan halittu kadai ita daga lahira take daga zatuakn annabi da imami ba zai taba yiwuwa su rabu da it aba, face a izinin Allah matsarkaki madaukaki, wannan shi ne banbanci tsakanin imamancinsu na halitta da shari’a da imamancinsu na duniya wanda ya ke da ma’anar mulki na zahiri kan mutane, mashi’ar annabi da imami biye take da mashi’ar Allah matsarkaki, idan Allah yaso ganin imami ko annabi matsayin wanda a kai galaba kansa cikin wani matsaya daga matsayu sai hakan ta kasantu cikin izinin Allah
(شاء الله أن يراك قتيلاً)
Allah ya so ganinka a kashe.
Wannan daga magi galibi kenan, kada ka gafala , idan imam ya so ka da ya sani lallai shi ba zai sani ba, duk da kasantuwa ya san dukkanin abin da ya kasance da abin da ya ke kasantuwa dama wanda zai kasance da izinin Allah matsarkaki, shi ilimin imami daga ilimin Allah ya ke sai dai cewa shi ilimin Allah a asali shi ilimi ne da babu jahilci ciki, shi kuma ilimin imami biye ya ke da shi sai dai cewa ya na tare da jahilci, idan Allah ya so ya sani take sai ya sani, idan kuma ya so kar ya sani toba zai sani ba.
Kamar wanda ya kasance mai gani sai ya so kada ya gani to lallai shi zai rufe idonsa sai ya zamanto ba zai ga abubuwa, ya halasta gare shi ya kore gani daga barin kansa, ya akasance mai gaskiya cikin fadinsa: shi imami cikin misalin wannan matsaya ko dai ya zama ya na da iko ko kuma sabanin haka, ma'ana ya cire kudura daga kansa da izinin Allah, k kuma dai ya kasance ya na da ikon amma bai amfani da ikon nasa,koma dai wanne ne ya kasance, lallai shi mai iko ne da ikon Allah, wakili ne kan dukkanin halittu da wilayar Allah matsarkaki, shi mai kewaya ne da duniya da abin da ke cikinta da bainda ke bayanta da izinin Allah matsarkaki, baki dayan duniya kewaye take da iliminsa da ikonsa, da wilayarsa ta tsarin halitta da izinin Allah matsarkaki, kamar yadda shi ne masani baki dayan duniya da abin da ke cikinta kuma shi ne mai iko kansu, Allah shi ne mai kewaya mudlakan, imami da annabi su kuma masu kewaya ne tare da kaidi, misalin wannan banbancin zai zama irin banbanci da ke tsakanin samuwa da rashi, hakama tsakanin wadatuwa mudlakan da talautuwa mudlakan, wannan ma'ana tana gasgatuwa cikin dukkanin siffofi da suke tajalli cikin kammalallen mutum ma'ana annabi da wasiyyi wanda mafhumin imamancin Allah ke tattara su da gamammiyar ma'ana da wilayatul uzma.
Na uku: walaya kulliya mudlaka kubra da uzma: lallai walaya da wasalin fataha kan wawun tana da ma'anar soyayya da kauna, amma da wasalin kisra tana zuwa da ma'anar mulki da hukumanci shi ne abin da mkue son bayani anan, wannan hukuma da sarauta wani lokacin ta na kasantuwa kayadaddiya kebantatta da zamani da bigire, wani lokacin kuma bata da kaidi zamani ko bigire, wannan a asali da idlaki da fi'iliya ga Allah matsarkaki madaukaki, shi ya ke da hakkin walaya da gaskiya, babu wnai kwatankwacinsa cikin zatinsa da siffarsa da ayyukansa, babu wanda ya sanya mene ne shi face shi bashi da abokin tarayya cikin dukanin siffofinsa na jalala da kamala da kyawu, bas hi da abokin tarayya bijire cikin walayarsa da mulkinsa, sai dai cewa wlayarsa tana tajalli cikin halittarsa mikewa da tsaho, kamar yada haskensa ya yi tajalli kan dutsen musa abokin zancen Allah sai musa ya fadi a sume.
﴿وَلَمَّا جَاءَ مُوسَى لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنظُرْ إِلَيْكَ قَالَ لَنْ تَرَانِي وَلَكِنْ انظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنْ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي فَلَمَّا تَجَلَّى رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكّاً وَخَرَّ مُوسَى صَعِقاً فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ﴾ (الأعراف: 143).
Lokacin da musa ya je mikatinmu ubangijinsa ya yi magana da shi ya ce ubangiji ka nuna mini inyi duba zuwa gare ka sai ya ce ba zaka ganni ba sai dai cewa ka dubi dutse idan ya tabbata a bigeransa da sannu za ka ganni lokacin da ubangiji ya yi tajalli kan dutse sai ya sanya shi nikakke musa ya fadi a sume lokacin ya farfado sai ya ce tsarki ya tabbatar maka ni ne muminai.
Wannan daga tajalli mai girma ga musa badadin Allah kenan amincin Allah ya kara tabbata gare shi, amma tajalli mafi girma kadai dai ya na cikin manzon Allah mafi girma muhammadu Mustafa, lallai walaya kulliya wacce take tajalli cikin halittu hakika da farko ta fara tajalli cikin masoyin Allah Muhammad ibn Abdullah, kamar yadda ya zo cikin addu'ar daren aiko shi annabi ishirin da bakwai ga watan rajab, muna rokon Allah matsarkaki da tajallinsa mafi girma cikin aiko manzonsa mafi karamci da ya gafarta mana zunubanmu ya sanya mana albarka ya karbi ayyukanmu ya yaba kyawawan ayyukanmu ya lullube munana nan ayyukanmu ya faranta zukatanmu ya bubbugo da arzikinmu.
Wannan tajalli mafi girma da hasken Allah mafi cika shi ne hasken nan da sarkin mumunai Ali (as) ya ke rantsuwa da shi cikin du'a'u kumaili
(وبنور وجهك الذي أضاء له كل شيء)
Da hasken fuskarka wanda komai ya haskaka da shi.
Haka ma ya zo cikin du'a'u sahar ta watan Ramadan:
(اللّهم إني أسألك بنورك من أنوره وكلّ نورك نيّر اللّهم إني أسألك بنورك كلّه).
Ya Allah lallai ni ina rokonka da haskenka daga mafi haskakarka da dukkanin haskenka mai haska ya Allah ina rokonka da baki dayan haskenka.
Wannan tajalli na farko wanda komai ya haskaku da shi shi ne mai tattaro baki dayan jam'in sunayen kyawawa da madaukakn siffofinsa, lallai duk da cewa ya kasance cikin duniya imkani basidi kwaya daya sai dai cewa shi ya kasance mai tattaro baki dayan duniyoyin samuwa da martabobin imkaniya lallai shi anayi masa lakabi da lakubba masu tarin yawa ta fuskanin da ya nayi mai yawa kamar misalin rahamar Allah mai yalwa, rahama ga talikai, da furkar Allah da kofar Allah, lallai hakikara ba murakkaba bace, shi samamme ne mudlaki wanda kae keto haskensa daga mudlakin samuwa daga hasken wajibul wujud ga zatinsa Allah shi ne hasken sammai da kasa, sannan ya kasantar da tsanin kwararar faira tsakanin mahalicci da halittu, lallai shi wannan tsani kasan mahalicci ya ke amma ya na saman dukkanin halittu, ana kiransa da halitta
(لا فرق بينك وبينهم إلّا أنّهم عبادك ففتقها ورتقها بيدك)
Babu banbanci tsakaninka da su face cewa su dai sun kasance bayinka hade su da raba su na hannunka.
ziyaratul, da samuwarsa matsarkaki hakikar halittu take bayyanuwa, ba don wannan tajalli mafi girma ba da ba a san Allah ba da kuma ba a bauta masa ba
(بنا عرف الله وبنا عبد)
damu aka san Allah damu aka bauta masa.
haka ya zo cikin hadisi kudusi:
(كنت كنزاً مخفياً فأحببت أن أُعرف فخلقت الخلق لکي أعرف)
Na kasance taska boyayya sai na so a san ni sai na halicci halitta domin a san ni.
Kadai dai muna sanin Allah ta hanyar sunayensa da siffofinsa, amma zatin Allah babu wanda ya san hakikaninsa sais hi girmansa ya girmama, dukkanin halittu iyalin tajallin annabta ne mafi girma, abin da ake ishara zuwa ga sunayen Allah da siffofinsa kadai shi bisa la'akari da tajalli mafi girma ne, amma saman haka da abin da ya ke bayansa shi mukamin zati ne wanda ake kiransa da lahutiyya, shi gaibun gaibu ne cikin mukamin dayantuwa, babu suna cikinsa babu zayya nawa wanda ake kiransa da huwa (shi) babu wanda ya san mene ne shi face shi girmansa ya girmama, sai ya yi tajalli cikin littafinsa mai tsarki rubutacce kamar yadda ya yi tajalli cikin halittarsa da littafinsa kasantacce, haka zalika muhammadu da iyalinsa da kur'ani da littafi aini, kadai dai dukkanin hakan ya kasance daga wancan tajalli mafi girma daga haskensa zuwa haskensa, daga gare shi zuwa gare shi, da shi ne ya ke kwararar da samuwa ta asali kan mahiyya abar la'akari sai ka kasance haifaffe, wannan shi ne abin da ake kia da samuwa shimfidadda, dukkanin girma da haiba daga grimansa, dukkanin kyawu da debe haso daga kyawunsa , da dukkanin kamala daga kamalarsa, da dukkanin haske daga haskensa
(اللّهم أني أسألك من بهاءك بأبهاه، وكلّ بهاءك بهيّ اللّهم إني أسألك من بهاءك كلّه)
Ya Allah ina rokonka daga haskenka daga mafi haskakarsa* da dukkanin haskenka mai haske ya Allah ni ina rokonka daga dukkanin haskenka.
Kamar yadda ya ke tabbatacce cikin nazariyyar hikima muta'alita karkashin ka'idar imkanul ashraf.
Wannan tajalli mafi girma da walaya mafi girmama da babbar shiriya tana yin tajalli cikin zamaninmu har zuwa ranar bayya nar maulanmu imamin zamaninmu hujja mafi cika bakiyatullahi a'azam hujjatu ibn hassan askari (as) wanda muke murnar haihuwarsa mai alabarka cikin tsakiyar watan sha'aban mai girma cikin kowacce shekara muke kuma sauraro da tsimayin bayya narsa da tsayuwarsa domin ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika da zalunci da danniya ya Allah ka gaggauta bayyanarsa ka saukaka fitowarsa, ka sanya mu daga tsarkakakkun shi'arsa da mataimakansa da masu tallafa masa masu shahada a gabansa amin amin karshen maganarmu lallai dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin talikai tsira da amincin Allah su kara tabbata ga muhammadu da iyalansa tsarkaka.