sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    Labarun da ba tsammani

    Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi

    Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi

    da sunan Allah mai rahama mai jin kai

    Imam mahadi (af) da tsawunta rayuwarsa cikin sabuwar mahanga daga alkalamin sayyida adil alawi.

    Dukkanin godiya abbata ga Allah wanda ya halicci zamani ya sanya cikinsa imami mai yanke uzuri, hujja mai hudar da bayani, tsira da aminci su tabbata ga mafi darajar halittu muhammadu da iyalansa imaman shiriya zababbu, musammam ma cika makin wasiyyai ma’abocin zamani Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja

    قال رسول الله  9: «من مات ولم يعرف إمام زمانه مات ميتةً جاهلية »،

    Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya mutu bai san imamin zamaninsa ba ya yi mutuwa irin mutuwa a lokacin jahiliya.

    Wannan hadisi shi’a da sunna sunyi ittifaki kansa.

    ka sani cewa lallai al’amarin imam mahadi hujja da ake saurare mai tsayawa wanda zai dawo daga tsatson iyalan muhammadu, imani da lamarinshi larura ne a duniyance da lahirance ba zai yiwu ayi inkarinsa ba, lallai da za ai inkarin batun imamul hujja to zai kasance kamar misalin mutane suyi inkarin makaginsu matsarkaki, lallai shi inkarin bai shiryawa zuwa ga rashin samuwarsa, kamar yadda inkarinsu ga ranar alkiyama haka bai nufin cewa ita kiyama ba zata tsaya ba babu hisabi.

    Al’amarin imam mahadi (as) wanda yake ya fito daga zuriyar manzon Allah (s.a.w) hakika ce tabbatatta, lallai wannan batu ya gangaro tun daga farko farkon muslunci ya kuma shahara tsakankanin musulmi a wancan lokaci har lamarin ya kai ga wallafa littafai masu tarin yawa tun karnin farko gabanin haifarsa (as) da shekaru

    Lallai ingantattun hadisai sun zo da hadisai masu daraja muwassakai daga manzon Allah musdafa mai bushara da gargadi muhammadu (s.a.w) da iyalansa tsarkaka : wanda sune daga sarkin muminai ali (as) sannan hassan almujtaba (as) sannan husaini shahidin karbala (as) sannan sai kuma imamai takwas daga `ya`yan husaini (as) dukkaninsu sunyi bushara da imam mahadi mai kawao gyara (as) da kuma cewa shi zai kasance cika makin wasiyyai kuma zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika da zalunci da danniya, akwai daruruwa daga riwayoyi da suke nuni kan wannan hakika da ba zai yiwu ayi inkarinta ba, kai bari ma dai ta wayi gari daga sallamammun abubuwa a tarihi da addinan sama daban daban sukai ishara zuwa gareta, kamar yadda ta kusa ta zama larura a hankalce, da cewa duniya da tayi bakir kirin da jahilci mai matukar duhu to ana jiran mai gyaranta mai haskakata da adalci da daidaito.

    Annabi mafi karamci (s.a.w) cikin daruruwan hadisai  sarkin muminai ali (as) cikin hadisai guda hamsin, Fatima zahara (as) cikin hadisai 3, imam hassan (as) cikin hadisai bakwai, imam husaini (as) cikin hadisai shahudu, imam sajjad (as) cikin hadisai takwas, imam bakir (as) cikin hadisai sittin da uku, imam sadik (as) cikin hadisai dari da talatin da hudu, imam musa alkazim (as) cikin hadisai goma, imam rida (as) cikin hadisai goam shadaya, imam jawad (as) cikin hadisai biyar, imam hadi (as) cikin hadisai shida, imam hasan askari (as) cikin hadisai ishirin da biyu.

    dukkaninsu sun shimfida hanya sauraron da yayewa da bayyanar ma’abocin zamani (af) da kuma kasantuwarsa cewa shi da sannu zai faku daga idanu cikin wani lokaci mai matukar tsayi da kafafuwa da yawan mutane zasu zame har lamarin ya juya ya kai ga kafirtarsu da inkarinsu da shakka da fadin cewa babu wata fa’ida cikin wannan fakuwa tasa, sai dai cewa manzo mafi karamci da imamai tsarkaka: sun ambaci fa’idar mai yawa cikin gajeriyar fakuwarsa da doguwar fakuwarsa – da kuma cewa shi hujja abin sauraro shi aminci ne ga kasa da samuwarsa sama da kasa suka tabbatu, albarkinsa ake azurta mutane, ba da ban shi ba da kasa ta niste da ahalinta, lallai shi kamar misalin rana ne a bayan labule, lallai shine mai shiryar da mutane cikin duniyar halitta, lallai shi yana lura da zukata da wilayar boye sai ya shiryar dasu zuwa ga tafarki madaidaci, lallai cikin kowacce shekara ya halartar taron Arafat duk da kasantuwarsa fakakke daga tsinkayar idanu, sai da yawa za a iya ganisa amma ba a sanshi kowaye ba. Sauraren bayyanarsa na daga cikin mafi darajar ayyuka, ya zama wajibi ga mai tsimayinsa ya yi cikakken tanadi, ya riki makami daga dukkanin abnda cikin akwai karfafa, ya tsimayi bayyanasa dare da rana, lallai duk wanda ke tsimayin hudar rana daga farkon dare ba zai wanzu cikin matsanancin duhu ba bisa fatansa na hudar rana bari dai zai kunna haske daga kewayensa koda kuwa da fitilar kendir ne da fitila kwai domin ya rayu cikin ni’imar haske sai ya dinga jin halartiwar rana ya tsimayeta domin ta bayyana ta haskaka baki dayan duniya.

    A mahangata siffanta imam mahadi (as) da rana da ya zo cikin riwayoyi cikinsa akwai ludufai, daga cikinsu: shine gabanin hudar rana dole dai a samu alfijir ya gabaceta da ido zai tanadin ganinta, lallai da zata haskako kai tsaye tsakiyar a tsakiyar sama lallai da haka zai haifar da makanta ga idanu zai kuma rikita tsari, dole dai ace an fara samun alfijir ya gabata sannan bayyanar rana sannu sannu sai kuma alfijir na gaskiya yay a kasance a kan ufuki ya dira kan ufukin gabas gabaninsa kuma alfijir din karya ya riga dama ya gabata, shi amudi ne kamar jelar kura, gabanin hudar ranar imamanci da wasicci dole ne a samar da alfijir din gaskiya da hukumar muslunci da za ta shimfida hanya, sannan za a samu da’awaowi mahadanci na karya daban daban a tsawon tarihi  wanda amudinsa kamar alfijr din karya yake. sai a lura. kamar yadda rana take amfanarda kasa ko da kuwa ranar hadari ya katangeta, sannan dole ne lokacin da ranar za ta hudo sai hadari yan kwansare ya kau da kadan kadan a tsakankaninsa zaka samu ranar ta fesa haskenta ta hudo zuwa kan kasa, wanda ya kasance yana raye kan kasa zai farin ciki da haskakarta da kyalkyalinta, zai yi kuma fatan kara hudowarta da haskowar a nan gaba, tsakanin zamani zuwa wani zamani kai hatta a kowanne zamani mutane na Imani da bayyanar ma’abocin zamani (as) cewa shi zai bayyana a zamaninsa kamar yadda muka shaida haka cikin wasiyyar sayyid ibn dawus ga dansa muhammadu gabanin shekaru dari bakwai da suka fgabata cikin littafinsa mai suna (almahajjatu fi samaratil bahajati) da cewa babu kokwanto sai dansa ya riski daular imam mahadi (as) ya kuma nemi da idan lokacin ya yi ya isar da sakon gaisuwarsa ga imam ya kuma sumbaci hannayensa, wannan na nufin cewa: imamai cikin ba da labarinsu kan alamomin bayyanar imam da tabbatuwarsu kan tsawon zamani sun nufi wanzarda tushen tsimayin imam mahadi (af) ta kasance mai haskaka cikin zukatan muminai ta yadda fata kan bayyanar ba zai kai ga ya mutu ba cikinsu, bari dai zasu kasance masu yakar zalunci da danniya da dawagutai da msu girman kai, su kasance masu tsimayin ranar kubuta da zamani bayyana cikakka, hakika mai tsayuwa ka’im daga iyalan muhammadu: kamar misalin rana yake kuma duk anda ke tsimayinsa cikin duhu da zalunci lallai shi a darensa na farko mai tsananin duhu ba zai kasance ya yardarma kansa rayuwa cikin duhu ba da hai zai kaiga ya dinga tuntube da abubuwa da zai kai gaya fada cikin ramin da ke kan hanyar rayuwarsa ya halaka, bari dai zai haskaka gabansa ko da kuwa da hasken fitilar kendir ne domin hanyar da yake ta kasance  cikin haske, sannan kuma zai wanzu cikin tsimayin hudar rana da tsimayi bayyana, lallai hakan ne mafi fifitar ayyuka, wanda yake imani da mahadi da bayyanarsa lallai zai gyara duniya da adalcinsa da hukumarsa kuma lallai zai zama kaya a idon makiya muslunci  da `yan mulkin mallaka da ma’abota girman kan duniya tareda bataloliyinsu gabas da yamma.

               A tsawon tarihi da zamanunnuka  duk wanda ke jiran imam kadai yana jiran cikar alkawalin Allah madaukaki wanda ya rike shi ya karfafa shi da alkawalinsa da ya lamuntar da shi, a tsawon tarihi ya kasance ya cudanya da zalunci da barna dukkanin wanda aka zalunata ya na jiran mai daukar masa fansa da zai karbar msa hakkinsa, dukkanin addinai da mazahabobi  suna tsimayin mai kawo gyara da kammala su, kadai dai shi’a imamiyya sun fifita daga wasunsu daga mazhabobi da cewa su sun san wannan mai kawo gyara a baki dayan duniya hakikanin sani, a wurinsu yana raye yana azurtuwa, yana rayuwa a tsakaninmu muna jin halartarsa muna kiransa muna ziyartarsa da ziyarar alu yasin, da misalin wannan mumini ke daukaka ya kusanci ubangijinsa da tsarkake kansa da tarbiyartar da ita, ya haskaka daga hasken imaminsa ya tsawon daga fairarsa da tsarkinsa ya rayu cikin fata ya yi kai kawo domin samun mafi falalar rayuwa wadda adalci da jin kai ke jagoranta, lallai yadda lamarin yake dukwa nda ya bai Imani da imam mahadi (as) zai fuskanci rarrawa da rashin tabbataci da hayaniya a duniya, lallai zai rasa samun dadin rayuwa da farin ciki zai jarrabtu da halaka kansa, kamar misalign wanda ke cikin jirgi a tsakiya guguwa mai tsanani zai kasance yana debe tsammani daga kai wa bakin gaba, lallai sallama kansa ga mutuwa ba zai yunkurin tseratar da kai ba, sabanin wanda yake da yakini cewa akwai wata bakin gabar kubuta da aminci, lallai wannan tareda tsananin guguwar igiyar ruwa ba zai sallamawa ba zai ta yunkurin kubuta da kaiwa ga aminci. Wannan na daga abinda larura da zahiri ke nuni zuwa gareshi.

    fatan rayuwa na lazimta yin tunani ingantacce da fafutika da taimakekeniyar zamantakewa da samar da sauyi da baki dayan mutane za su yi tarayya cikinsa, da kuma dauki babu dadi mara yankewa da samar da yanayi da kawar da dukkanin matsaloli da ke zama shinge kan hanya    

    da misalin wannan kuduri da akida da fata shi’anci ya rayu har zuwa wannan zamani da muke ciki tareda dukkanin tsanani da danniya da kisa da dauri da azabtarwa da mabiyansa wandada suka gabace suka  fuskanta daga sarakuna makiya ahlul baiti (as) a tsawon tarihi imamin jafar sadik (as) yana cewa: duk wanda yam utu yana mai tsimayin wannan lamari daidai yake da misalign wanda ya kasance tareda imam mahadi cikin hemarsa, bari dai misalinsa kamar wanda ya yi yaki da takobi tareda manzon Allah (s.a.w) ya zama wajibi ga mai sauraro ya shimfida hanya ya samar da gada ga ranar bayyana ya ksance kamar wanda ya yi tanadi yana jiran bakonsa, sai ya zamanto ya tsaftace gidansa ya yi shiri tsaf don tarbar liyafarsa, duk wanda bai aikata haka zai kasance abin zargi a wurin ma’abota hankula, ana kidiya shi cikin wanda suka fadi basu samun nasara ba cikin rayuwarsu, zai rasa nutsuwa da dacewa za fada cikin gigita da bata.

    Ya zo cikin littafin kamaluddini da isnadinsa daga jabir ibn Abdullah Ansari ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: mahadi daga `ya`yana sunansa irin sunana alkunyarsa irin alkunyata, shine yafi kowa kama dani cikin halitta da dabi’a fakuwa za ta kasance gareshi da gigita da al’ummu za su bata cikinta sannan zai gabato kamar misalin tauraro mai huda zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da danniya.

    daga cikin littafin dai da isnadinsa daga sudairu daga baban Abdullah (as) ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce farin ciki ga wadanda suka riski mai tsayuwa daga ahlin gidana wadanda suka kasance suna kwaikwayonsa gabanin tsayuwarsa suna binsa suna bin imaman shiriya gabaninsa suna barranta zuwa ga Allah mai girma da daukaka daga makiyansu. lallai wadanan sune abokaina mafi karamcin al’ummata a gurina.

       daga cikin littafin kamaluddini da isnadinsa daga husaini ibn khalid daga ali ibn musa rida (as) daga iyayensa masu karamci (as) daga sarkin muminai ali ibn dalib (as) ya cewa husaini (as) mutum na tara daga `ya`yanka ya husaini shi zai kasance ka’im (mai tsayuwa) kan gaskiya mai bayyanar da addini mai shimfida adalci. Sai husaini ya ce: n ace masa ya saerkin muminai yanzu hakan zai kasance kuwa? Sai ya ce: eh na rantse da wanda ya aiko muhamadu da annabta ya fifita kan dukkanin mutane, sai dai cewa bayan fakuwa da dimauta babu msau samun tabbatuwa a kan addini face tsarkakakku wadanda suke alaka kai tsaye da ruhin yakini Allah ya riki alkawalinsu da wilayarmu ya rubuta imani cikin zukatansu ya karfafesu da ruhi daga gareshi.

     Daga cikinsa da isnadinsa daga abu basir ya ce: naji baban Abdullah (as) yana cewa: lallai daga cikin sunnonin annabawa da abinda ya afku da su daga fakuwa za ta faru da imam mahadi ka’im daga ahlul baiti (as) sawu da sawu dai da dai, sai abu basir ya ce: ya `dan manzon Allah wanene ka’im daga ahlul baiti?

    Sai ya ce: ya abu basir shine mutum na biyar daga zuriya `ya`yan musa, wadancananka shi `dan  shugabar bayi ne zai faku fakuwar da batattu za su yi kokwanto, sannan Allah mai girma da daukaka ya bayyanar da shi ya kuma bude gabas da yamma a hannunsa. Ruhullah isa `dan maryam zai sauko  yai sallah a bayansa kasa za tai haske da hasken ubangijinta, wani bigire ba zai rage ba a kan doron kasa ana bautar wanin Allah, addini baki dayansa zai kasance ga Allah ko da kuwa surikai basa so.

    Muna da gomomin riwayoyi da daruruwan misalign wadannan hadisai masu daraja wadanda ke dasa fata cikin zukata haka akwai tarin riwayoyi da suke nuni kan cewa kasa ba zata taba fakuwwa babu hujjar Allah ba.

    daga abanu ibn taglib ya ce: baban Abdullah (as) ya ce: hujja gabanin halittta tareda halitta bayan halitta.

    wannan na nufin cewa lallai hujja da dalili daidai suke da sababi da musabbabi da izinin Allah matsarkaki da kuma sune illar makasudi ta nan gaba da ta yanzu ga halittu, lallai hujja na bayyanuwa da ayyanuwa cikin imami ma’asumi (as) mafi game daga ya kasance annabi ko wasiyyi.

    yazo cikin littafin ikmal da isnadinsa daga abi Hamza sumali daga baban Abdullah (as) ya ce: na masa: shin kasa zata wanzu ba tareda imami ba? Sai ya ce: da kasa zata wanzu ba tareda imami `dan wani lokaci da ta halaka.

    Ya zo cikin alkafi da isnadinsa daga Abdullah ibn sulaiman al’amiri daga baban Abdullah (as) kasa bata taba gushewa face cikinta akwai hujjar Allah da ya san haram da halal yana kuma kiran mutane ya zuwa tafarkin Allah.

    Ya zo cikin kamaluddini da isnadinsa daga Ibrahim ibn abi mahmud ya ce: imam rida (as) ya ce: mune hujjojin Allah cikin halittunsa mune halifofinsa  cikin bayinsa amintattunsa kan sirrikansa, mune Kalmar takawa mune karfaffar igiya, mune shaidun Allah da tutocinsa bayinsa, damu Allah ya damke sammai da kasa daga zamewa, damu Allah ke saukar da rayuwa da yada rahama, kasa ba zai taba yiwuwa ta gushe daga mai tsayuwa daga garemu a bayyane yake ko a boye, da zata wofinta daga hujja da ta yi wurgi da wadanda ke cikinta kamar yadda kumfar kogi ke wurgi da abinda ke cikinsa,

    Ya zo cikin alkafi da isnadinsa daga Hamza ibn dayyar ya ce: naji baban Abdullah (as) yana cewa da ace babu wanda suka wanzu a doron kasa face mutum biyu da Allah ya sanya dayansu hujja.

    Imam (as) ya ce: karshen wanda zai mutu shi imam, don kada wani mutum ya kafawa Allah mai girma da daukaka hujja da cewa ya barshi ba tareda hujjarsa.

    Tsarin halitta da na shari’a cikin wanzuwarsa yana bukatuwa ya zuwa ga hujja mafi girma ta Allah da faira mafi tsarkaka na ubangiji, iradar Allah ta ratayu da ya kasance cikin wanzuwar tsarin halitta dana shari’a kadai ya dogara da samuwa da imami ma’asumi da ma’ana mai gamewa da yake misaltuwa cikin annabi da wasiyyi (as)

    Sarkin muminai ali (as) cikin nahjul balaga yana cewa:  tabbas  kasa bata wofinta daga hujjar Allah, ko dai bayyananne shahararre, ko dai wanda ke cikin tsoro a boye, domin kada hujjojin Allah su ruguje, nawa daga wannan ina wadannan suke? Wadannan hujjoji wallahi sunada karancin adadi sunada girman matsayi, Allah yana kiyaye hujjojinsa da su a shaidunsa har ya sanyasu tamkarsu ya dasa su cikin zukatan makamantansu, da su ilimi ya mamaye hakikanin basira, su kai mubashara da ruhin yakini, suka tsausasa abinda mabarnata suka ruruta

    Suka debe haso daga abinda jahilai suka gigita, suka zauna da duniya da jikkuna da suke rataye a madaukakin muhalli, wadancananka sune halifofin Allah a doron kasarsa sune masu kira zuwa addinin Allah.

      Imam (as) cikin wata hudubarsa ya ce: sune karamomin kur’ani sune taskokin Allah in sunyi furuci sai su fadi gaskiya idan sukai shiru ba a gabatarsu.

    A wani wajen kuma ya ce: da su gaskiya ta dawo cikin muhalllinta da su karya ta gushe daga muhallinta harshenta ya yanke daga tushensa sun hanakalta da duniya hankaltar wayewa da kiyayewa, bawai hankaltar ji da kunne ba da rawaita lallai marawaita ilimi na matukar yawa amma masu kiyaye shi suna da karanci.

    Imam abu jafar albakir (as) ya ce: wallahi Allah bait aba barin doron kasa ba tareda da hujja ba tunda ya karbi ran adamu (as) face sai ka samu imami cikinta da ake shiriya da shi zuwa ga Allah shine hujjar Allah a kan bayinsa kasa ba ta wanzuwa ba tareda hujjar Allah ba a kan bayinsa.        

    Imam sadik (as) ya ce: wasiyyai sune kofofin Allah wadanda daga garesu ake zuwa wurinsa ba da ban su b aba za a son Allah ba da su Allah ya kafawa bayinsa hujja.

    Imam (as) ya ce (lallai Allah ya halicce mu ya kyawunta surar halittarmu ya sanya mu taskokinsa cikin samansa da kasansa, da mune bishiya ta yi Magana da ibadarmu aka bautawa Allah bada ban muba da ba a bauta masa ba.

    Daga abu khalid kabili ya ce: na tambayi baban jafar (as) daga fadinsa madaukaki:

    (فَآمِنوا بِاللهِ وَرَسولِهِ وَالنُّورِ الَّذي أنْزَلـْنا)

    Sai sukai Imani da Allah da haskenda muka saukar.

    Sai ya ce: ya abu khalid wallahi wannan hasken imamai ne, ya abu khalid hasken imami cikin zukata yafi haskaka daga hasken rana mai haskaka da tsakar rana, sune masu haskaka zukatan muminai, Allah yana shngance haskensu ga barin wanda ya so, sai zukatansu suyi duhu ya lullubeta da wannan duhu.

    Akwai daruruwan riwayoyi da nassoshi daga hadisan annabi da imam da kuma dalilan hankali da suke nuni kan samuwar kammalallen mutum daga dukkanin kamala daga ma’ana, yana rayuwa kan doron kasa shine igiyar sadarwa tsakanin duniyar gaibu (boye) da duniyar bayyane, fairar Allah na saukowa gareshi domin ya yada ta zuwa talikai, albarkacinsa ake azurta dukkanin mutane da samuwarsa ne kasa ta tabbata, lallai rashinsa a doron kasa na nufin halakarta da karewar nau’in dan adam sakamakon koruwar manufa da hadafi da ake nema, shine sirrin samuwa  wanda ta hnayarsa ake sanin samuwa tsantsa. Duk abinda za a fada kansa gameda bai wuce daya bisa goma ba dan adam ya gaza sanisa hakikanin saninsa.   

    Wannan Kenan, hujjar Allah mafi girma a zamaninmu kadai dai shine ma’abocin zamani baban salihu ka’im muntazar jarumin hijaz imami na goma shabiyu  daga imaman shiriya tutocin takawa rukunan gari shugabanni bayi, wannan shine majibancinmu da lamrinmu mahadi daga iyalan Muhammad: wanda hadisai mutawatirai sunzo daga annabi muhamadu musdafa da iyalansa  tsarkaka daga makarantar shi’a da sunna.

     manzon Allah (s.a.w) ya ce: duniyar ba zata tafi ba har sai wani mutum ya shugabanci al’ummata daga iyalan gidana ana kiransa mahadi.

    Ya ce: kuyi bushara da mahadi,(sai da ya maimaita fadin haka sau uku) zai fito lokacinda mutane suke cikin sabani da girgiza mai tsanani zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da danniya, zai cika zukatan bayinsa da ibada ya yalwacesu da adalci.

    Ya ce: kiyama ba za ta tsaya ba har sai mai tsayuwa da gaskiya ya tsaya, hakan zai kasance lokacin da Allah mai girma da daukaka ya yi masa izinin fitowa, duk wanda ya bishi ya kubuta duk wanda ya juya masa baya ya halaka, ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah yaku bayin Allah ku je wajensa ko da ko a kan dusar kankara ne lallai shine halifan Allah mai girma daukaka kuma halifana.

    Ya ce: duk wanda ya yi inkarin mai tsayuwa daga `ya`yana hakika ya yi inkarina.

    Ya ce: duniya ba zata tafi ba har sai wani mutum daga `ya`yan husaini ya tsayu cikin lamarin mutanena, zai cika da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya.

     sarkin muminai ali (as) ya tamabayi manzon Allah (s.a.w) ya ce: ya manzon Allah shin mahadi daga cikinmu yake  ko daga cikin wasunmu? Sai manzon Allah(s.a.w) ya ce a a daga cikinmu yake da shi Allah zai cika addini kamar yadda damu ya bude addini, damu Allah yake tseratarwa daga fitina kamar yadda ya tseratar dasu daga shirka, damu Allah yake tattaro tsakanin zukata ya hadasu bayan gabar fitina su zamanto `yan’uwa kamar yadda ya hada tsakaninsu bayan gabar da kiyayyar shirka suka wayi gari `yan’uwan juna cikin addininsu.

    Ya ce: mahadi daga tsatsona ahul baiti yake zai fiton a karshen zamani sama za ta saukar masa da digon ruwanta kasa za ta fito masa da abinda aka shuka mata, zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda mutane suka cika ta da zalunci.

     An karbo daga ummu salama tace: naji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: mahadi daga tsatsona yake daga `ya`yan Fatima.

    Ya ce: mai tsayuwa daga `ya`yana sunansa irin sunana alkunayrsa irin tawa halayensa irin nawa sunnarsa iri daya da tawa, zai tsayar da mutana kan addinina da shari’ata  zai kirasu zuwa ga littafin Allah mai girma da daukaka, duk wanda yayi masa biyayya ni yayiwa duk wanda ya saba masa ni ya sabawa, duk wanda yayi inkarinsa cikin fakuwarsa hakika yayi inkarina duk wanda ya karyatashi hakika ya karyatani, duk wanda ya gasgatashi hakika ya gasgatani, wurin Allah na ke kai karar masu karyatani cikin lamarinsa masu jayayya da maganata cikin sha’aninsa masu batar da al’ummata ga barin hanyarsa da sannu wadanda sukai zalunci zasu san wacce majuya zasu juya gareta.

    Daga abu ayyub Ansari ya ce: naji manzon Allah (s.a.w) yana cewa nine shugaban annabawa ali kuma shugaban wasiyyai jikokina sune mafi alherin jikoki, daga cikinmu imamai ma’asumai daga tsatson husaini suke daga cikin mahadi mai shiryar da wannan al’umma yake, sai wani balaraben kauye ya mike ya ce: ya manzon Allah imamai nawa ne bayanka? Sai ya ce: adadinsu adadin kabilun banu isra’il adadin hawariyawan annabi isa.

    Daga huzaifa ibn usaid daga annabi (s.a.w) cewa shi ya ce: imamai bayana adadinsu daya da adadin shugabannin banu isra’ila tara daga cikinsu daga jinin husaini suke, sai dai cewa su suna tareda da gaskiya, gaskiya kuma na tareda su ku duba yadda zaku halifantar dani cikinsu.

    Daga sa’id ibn musayyab daga umar ibn khaddab da usmanu ibn affan cewa su biyun sunce: munji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: imamai bayana goma shabiyu ne tara daga zuriyar husaini daga cikinmu mahadi mai shiryar da wannan al’umma yake, duk wanda yayi riko da su a bayana hakika yayi riko da igiyar Allah wanda kuma ya wofuntar da su hakika ya wofunta.

    Wannan daga hanyar shi’a Kenan amma daga bangaren sunna hakika littfansu cike suke da ire iren wadannan hadisai kai akwai babuka masu cin gashin kansu kan bayani kan mahadi cikin ingantattun littafanu.

     An karbo daga Abdullah ibn mas’ud ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: duniya ba zata tashi ba har sai wani mutum daga iyalan gidana ya mulketa wanda sunansa irin daya da sunana.

    Tirmizi ya ce wannan hadisi ingantaccene aliyu ibn sa’id ya rawaito shi da ummu salama da abu Huraira.

    Aliyu ibn abi dalib (as) ya rawaito daga manzon Allah (s.a.w) ya ce: da ace babu abind ya rage sai kwana day arak a duniya da Allah ya turo wani mutum daga ahlin gidana da zai cika duniya da adalci akamr yadda ta cika da zalunci.

    An karbo daga ummu salama tace: naji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: mahadi daga tsatsona yake daga `ya`yan Fatima yake.

    Imam bakir (as) yana cewa duk wanda ya kusanci Allah da wata ibada da ya wahaltar da kansa cikinta amma kuma babu imami cikinta to yayi wahalar banza, shi batacce ne dimautacce, Allah na kin ayyukansa, idan yam utu kan wannan hali ya mutu mutuwar kafirci da munafunci.   

    Manzon Allah (s.a.w) ya ce: a karshen zamani bala’I mai satnani zai sauka kan al’ummata daga sarkinsu ba a taba jin labara bala’in da ya fi shi tsanani ba, har sai ksa ta kuntata da su duk da fadadarta har sai ta kai ga ta cika makil da zalunci da danniya, mumini zai rasa inda zai fake daga zalunci sai Allah ya aiko wani mutum daga tsatsona ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da danniya, wanda ke zaune a sama zai yardarm da shi da ma wanda ke zaune a kasa, kasa ba zata togace wani abu daga abinda aka shuka mata face ta fito shi, haka ma sama ba zata bar wani digon ruwa ba face ta kwararar da shi kansuya na mai kwarara, zai rayu cikinsu shekaru bakwai ko tara matattu zasu burin rayuwar wadanda suke raye sakamakon abinda Allah ya bawa mutanen da ke doron kasa daga alherinsa.

    Da yawab yawn malaman ahlus sunna sun tabbatar da tawatirancin hadisan mahadi (as) sun yi rubutu da wallafe wallafe kan imam mahadi muntazar (as) kamar misalin ibn hajar haisami muta’assibi cikin littafinsa mai suna (sawa’ik muhurika) da shabalanji cikin (nurul absar) da malam kanji shafi’I cikin (albayan fi akbarul sahibuz zaman) da shaik Mansur  ali cikin (gayatul ma’amul) da suwaidi cikin saba’ik zahab) da ibn hajar askalani cikin (nuzhatun nazir) da shaik yusuf ibn yahaya shafi’I wanda yayi afati a 658 cikin (ikdul durari fi akbarul muntazar) da shaik hammud ibn Abdullah tuwaijiri cikin (al’ihtijaji bil asari ala man Ankara mahadi muntazar) da shaik Mustafa shibuli cikin (sahihul ashradul sa’a) da shaik abdul muhsin ibn hammad ibad cikin (akidatu ahlus sunna wal asar fi mahadi muntazar war raddi ala man kazzaba bi’ahadisil sahihatu waridatu fil mahadi) da shaik mohd ibn ahmad ibn ism’il mukaddam cikin ( almahadi hakikatu la kurafatu) da shaik abdul latif Ashur cikin (salasatu yantazuruhum alam isa, dajjal, mahadi) da shaik mohd ali sabuni cikin (ashradu sa’a) da shaik hammud ibn Abdullah tuwaijiri cikin ( ittihaf jama’a bima ja’a  fi fitani wal malahim  wa ashradu sa’a) da shaik jazza’au shimari cikin (alamat sa’a fl kur’ani was sunna) da shaik tuwaijiri cikin (ikamatul burhani fi raddi ala man Ankara kurujal mahadi wal dajjal wa  nuzulul isa fi akiril zaman) da shaik rufa’I sarur cikin (kuduratu da’awa) da doctor umar sulaimanu ashkaru cikin (yaumul akar kiyamatul sugra) da shaik aminu haji muhamadu ahmadu cikin (ashradul sa’a sugura wal kubura)  da ibn kasir cikin (nihayatul fitan akiril zaman) da hafiz abu isma’il ibn kasir shafi’i cikin (alfitanu wal malahim alwaki’a fi akiril zamani) da kuma cikin (alamatu yaumil kiyama) da doktor abdul baki ahmad muhammadu salama cikin (baina yadus sa’a) da abdul latif Ashur cikin ( masihu dajjal hakika la kiyal) da muhammadu ibn rasul shafi’I cikin (isha’atu ashradul sa’a) shaik ahmad ibn muhammadu ibn sadik cikin (ibrazul wahami almaknun min kalami ibn kaldun fi ahadisil mahadi) da salahuddini abdul hadi cikin (hakikatul kabar an mahadi muntazar) da shaik abdulllahi hajjaj cikin (kaulul fasali fi mahadi muntazar) da haisami cikin (kaulul muktasar fi alamatul mhadi muntazar) da abdul mu’udi abdul masud cikin (amahadi fil mizan) shaik nasiru dini albani cikin (silsilatu ahadisis sahiha) da muttaki hindi cikin ( Burhan fi alamat mahadi akirul zaman) da shaik aksara’I cikin (talkisul bayanfi alamat mahadi akiril zaman) da tahawuni cikin (alkidab malihu fi tahkiki mahadi wal masihu) da muhammadu ibn abdul azizi almani’u cikin tahkikul nazaru bi akbarul muntazar) da abu a’ala  maududi cikin ( bayanat) da ragowarsu daga magabatan da wanda suka zo bayansu daga malamai da wayayyu zamu tsaya anan don gudun tsawwalawa dalibi.