فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Alheri a luggance da Isdilahi

Alheri a lugga: yana daga (khara) ma'ana abin da mutum yake zaba sakamakon kyawunsa da kamalarsa saboda haka alheri shi ne samun abu kan kamalarsa sakamakon fa'idojin da suke kunshe cikinsa, sai dia cewa masdarin Kalmar alheri a hakika shi ne Allah matsarkaki, shi alheri ne tsantsa kuma tsantsar alheri, duk abin da ya kasance daga gare shi alheri kuma kyawunta ne, duk abin da kasance daga waninsa kamar misalin Shaidani sharri ne mummuna.

Sabida haka alheri a isdilahin muslunci: shi ne abind amutum yake zaba sakamakon halastaccen kyawunsa daya gangaro daga hukuncin wahayi da lafayayyen hankali ko kuma daga dayantacciyar halitta, shi alheri aiki ne nagari bawai abin da sha'aew-sha'awe da son kai da girman kai da abin da yayi kama da haka suke ishara zuwa gare shi ba, ta yiwu jama'ar da sha'awe-sha'awe sukai galaba a kansu ka same su su suna suranta sharri a matsayin alheri, kamar yanda suke suranta ma'arufi a matsayin munkari sannan munkari a matsayin ma'arufi, a wannan lokaci ya zama dole cikin banbance tsakanin sharri da alheri mu koma zuwa ga Allah matsarkaki da abin da yake fada daga sharri da alheri cikin littafinsa da shari'arsa kan harshen Annabawansa da Wasiyansu da Malamai nagargaru, lallai shi ne mafi sani cikin haka.

Allama Shaik Fakaruddini Adduraihi cikin Majma'ul Bahraini yana cewa: alheri shi ne fadinsa madaukaki: 

 (وَافْعَلُوا الْخَيْرَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ)1

Ku aikata alheri saranku kwa rabauta.

An karbo daga Ibn Abbas ya ce: aikata alheri ishara zuwa kan sadar da zumunci da aikata kyawawan halaye sai ya zamana kwadaitarwa ce kan sauran ayyukan mustahabbi da neman kusancin Allah matsarkaki.

Sannan fadinsa madaukaki:

 (فَاسْتَبِقُواْ الْخَيْرَاتِ)[2]

Ku yi rigegeniya zuwa ga aikata ayyukan alheri.

Ma'ana ayyuka nagargaru masu alheri.

Sannan wani lokaci alheri yana zuwa da ma'anar dukiya

(وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ)3

Lallai shi yana tsananin son dukiya.

(إِنِّيَ أَرَاكُم بِخَيْرٍ)[4]

Lallai ni ina ganinku da kudade

 (فَكَاتِبُوهُمْ إِنْ عَلِمْتُمْ فِيهِمْ خَيْراً)[5] 

 Ku daura musu fansa idan kun san akwai wani alheri daga garesu.

Ya ce idan kun san suna da dukiya.

Ya ce: Alheri shi ne ya shaida babu abu bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya kasance yana abin da zai samu riba a hannunsa.

 (فِيهِنَّ خَيْرَاتٌ حِسَانٌ)[6]

Cikinsu akwai kyawawan mata nagargaru.

Ance abin da ake nufi da Kayyirat idan ya zo da shadda shi ne mata masu kame kansu basa aika alfasha.

 (وَرَبُّکَ يَخْلُقُ مَا يَشَاء وَيَخْتَارُ مَا كَانَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ سُبْحَانَ اللَّهِ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ)[7]

Kuma ubagijinka yana halittar abin da ya so yana kuma zaba su mutane zabi baya garesu tsarki ya tabbata a gare shi ya daukaka daga abin da suke yin shirka da shi.

Ba boye yake ba wannan aya tana raddi kan wadanda suke tabbata da imamanci da zabi, sannan misalin wannan aya fadinsa

 (وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلاَ مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْراً أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ
أَمْرِهِمْ
)
[8] .

  Bai dace ga Mumini da Mumina idan Allah da Manzonsa suka hukunta wani lamari ace suna da zabi daga lamarinsu ba.

 (وَاخْتَارَ مُوسَى قَوْمَهُ سَبْعِينَ رَجُلا لِّمِيقَاتِنَا)[9]

Kuma Musa ya zabi mazaje saba'in domin mikati da mu.

Mai tafsiri ya ce: shi Iktiyar shi ne nufar abin da shi ne alheri, ana cewa alheri na tsakanin abubuwa guda biy sai ya zabi daya daga cikinsu, hakika cikakkaken bayanin ayar ya gabata cikin ra'ayi

وفي الحديث : خيركم خيركم لأهله وأنا خيركم لأهلي 

Ya zo a hadisi Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mafi alherin cikinku shi ne mutumin da ya kasance mafi alheri ga ahalinsa nine mafi alherin cikinku sabida ahalina.

Wannan hadisi yana ishara zuwa sadar da zumunci da kwadaitarwa cikinsa.

Shi alheri kishiyan sharri jam'insa a larabce (kuyur kayar ) daga cikinsa ana cewa jazahullahu kairan (Allah ya saka masa da alheri) alheri kamar yanda bayani ya zo a littafin Ma'ani Akbar na Shaik Saduk wata korama ce a cikin Aljanna tana fita daga Kausar ita kuma Kausar tana fitowa daga Al'arshi, a kanta ne matsugunan Wasiyyai suke sannan shi'arsu suna gefan wannan Korama ga tsirrai duk sanda aka sare daya daga cikin sai wanbi sabon tsiro ya hudo hakan ya kasance daga fadin Allah (cikinsu akwai kyawawan mata) idan mutum ya cewa abokinsa Allah ya saka maka da alheri abin da yake nufi shi ne Allah ya bashi daya daga cikin wadancan matsugunai da Allah Ta'ala  yayi tanadinsu

Wani mutum ya aika da wasika zuwa ga Husaini Ibn Aliyu (a.s) yana cewa: ya shugabana ka bani labari gameda alherin duniya da lahira? Sai ya aika masa da amsa: da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai, bayan haka: lallai duk wanda yake neman yardar Allah da fusata mutane Allah zai isar masa cikin lamurran mutane, duk wanda yake neman yardar mutane da fusata Allah Allah zai sallama shi ga mutane ya barshi da su.

Ya zo cikin hadisi: anyi tambayi Imam (a.s) menene alheri? Sai ya ce: alheri bashi wai `ya`yanka da dukiyarka su yawaita ba sai dai cewa alheri shi ne iliminka ya yawaita, hakurinka ya girmama, ka yiwa mutane kwarjini da bautawa ubangijinka, idan ka kyautata ka godewa Allah, idan kuma ka munana ka nemi gafararsa.

Su mutane mafi alheri kishiyar Ashararai ne, mace mafi alheri ma'ana mai falala da daraja da kyawun halaye, namiji mafi alheri ma'ana ma'abocin alheri, idan akace Kayyirat ana nufin masu aikata alheri.
ya zo cikin addu'a: (kaine mahaliccin alheri da sharri) ance ma'ana ya daga halittar ta kaddarawa ba ta kasantarwa b, ma'ana Allah ya na kaddara alheri kamar yanda yake kaddara sharri, bawai yana aikata sharri ba, ya ce masa kasance sai ya kasance, hakika Allah ta'ala mai iko ne kan aikata munnana da sharri sai dai cewa baya aikata, domin aikata sharri na ksancewa sakamakon jahilci shi kuma Allah masanin komai ne, ko kuma dai sakamakon gazawa da kasawa shi kuma Allah mai iko ne kan komai, kamar yanda hakan ya tabbata cikin ilimin Tauhidi.

Ya zo cikin hadisi:

«تخيّروا لنطفكم فإنّ العرق دسّاس» 

ku zabi ku gwangwaje zabi domin tsatsonku lallai jijiya tana naso.

Ma'ana ku zabi abin da yake alheri da tsarkaka ku nesanta tsatsonku daga matayen banza Fajirai

«وإيّاكم وخضراء الدّمن المرأة الحسناء في منبت سوء».

Na haneku da furen juji kyakkyawar mace daga tushe mara kyawu.

Sai fadin Imam Zainul Abidin cikin shaharariyar hudubarsa a fadar Yazidu (ni `da ne daga mafi alherin mutane) daga larabawa da Ajamawa. Da kuma fadin Manzon Allah (s.a.w): (ina tsakanin zabi biyu) tsakanin yin istigfari neman gafara da barinsa cikin fadin Allah ta'ala: 

 (اسْتَغْفِرْ لَهُمْ أَوْ لاَ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ).

Ka nema musu gafara ko kuma kada ka nema musu.

Ana cewa karallahu laka ma'ana ya baka mafi alheri gareka (istikara) neman abin da yake alheri.

Ya zo cikin hadisi:

«استخر ثم استشر» 

Kayi istihara sannan ka nemi shawara.

Ma'ana ka nemi abin da yake mafi alheri daga Allah kace:

 «اللّهم إنّي استخيرک خِيَرة في عافية»

Ya Allah ina neman zabinka na laheri cikin lafiya.

Ka maimaita karantawa sannan daga baya sai kayi shawara, lallai idan ka fara da Allah zai zartar alheri gareka kan harshen wanda ya so daga halittunsa.

 Ka zaba mini alheri ka kimsa mini aikata shi ka zaba mini mafi gyaruwa, wannan shi ne zabi na daga abin da yake kasancewa Allah ne mai zabi.

Alheri yana zuwa don fifiko, sai ace: ai shi ya fi alheri daga wannan,yana zuwa a suna fa'ili ba a nufin fifiko cikinsa  (sallah iatace alheri daga bacci).

Ya zo cikin littafin Mufradatul Alfazil Kur'anil Karimi na Malam Ragibul Isfahani cikin Kalmar Alkairu ya ce: shi Alkairu shi ne abin da kowa da kowa yake kwadayi cikinsa kamar hankali alal misali da adalci da falala da abu mai amfanarwa, kishiyarsa shi ne sharri, ance shi alheri kala biyu ne: Mudlaki shi ne wanda ake kwadayinsa a kowanne hali wurin kowa da kowa kamar yanda amincin Allah ya tabbata a gare shi ya siffanta Aljanna ya ce:

«لا خير بخير بعده النّار، ولا شر بشرٍ بعده الجنّة».

Duk wani alheri da wuta ta biyo bayansa ba alheri bane, duk wani sharri da Aljanna ta biyo bayansa ba sharri bane.

Alheri da sharri abubuwa ne biyu da suke da dabaibayi: ta yiwu abind ayake alheri ga wane amma a wurin wane sharri kamar misalin dukiyar da take alheri ga Zaidu ta zama sharri ga Amru, sabida hakane Allah ya siffanta shi da abubuwa guda biyu ya ce: (idan ya bar wata dukiya) a wani wurin kuma ya ce:

 (أَيَحْسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِ مِن مَّالٍ وَبَنِينَ * نُسَارِعُ لَهُمْ فِي الْخَيْرَاتِ)

Shin suna tsammanin kadai muna karfafa su da shi daga dukiya da `ya`ya*muna gaggauta musu cikin alherai.

Fadin Allah ta'ala (in taraka kairan) kairu anan wurin ya zo da ma'anar dukiya, wasu ba'arin Malamai sunce ba a kiran dukiya da sunan kairu sai idan ta kasance mai tarin yawa daga tsarkakakken wuri, kamar yanda aka rawaito daga Aliyu (a.s) ya shiga wajen wani masoyinsa sai ya ce: yanzu bana yi wasiyya ba ya Sarkin Muminai? Sai Imam ya ce, a a ba zaka yi ba sabida Allah ya ce: (idan ya bar dukiya mai tarin yawa) kuma kai baka da wannan dukiya, kan wannan aya ta zo: (lallai shi yana tsanantawa kan son alheri) ma'ana dukiya mai tarin yawa.

Wasu ba'ari daga Malamai sun ce: dalilin da yasa ake kira dukiya mai yawa anan da sunan alheri tanbihi ne kan tausasa- shi ne abin da yake kyawunta ayi wasiyya da shi ai abind aya kasance daga wasu adadi na kudade daga fuska mai kyawu, kan wannan fadinsa madaukaki:

 (قُلْ مَا أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَالِدَيْنِ)

Abin da kuka ciyar daga alheri ga iyaye yake.

 (وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللّهُ)

Abin da kuka aikata daga alheri Allah yana sane da shi.

  (فَكَاتِبُوهُمْ إِنْ عَلِمْتُمْ فِيهِمْ خَيْراً)

Ku kulla alkwari dasu idan kun san cewa akwai alheri tare da su.

Ance idan kun san cewa suna da kudi, wasu kuma suka ce idna kun san cewa `yantar dasu zai dawo kanku da kansu zai amfanar

Shi alheri da sharri ana fadinsu daga fuska biyu:

Ta farko: su kasance sunaye ne guda biyu kamar yanad aya gabata shi ne fadinsa madaukaki:

 (وَلْتَكُن مِّنكُمْ أُمَّةٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ)

Ya kamata cikinku wata al'umma da zata dinga kira zuwa ga alheri ta kasance.

Fuska ta biyu: su kasance siffofi biyu bisa kaddara (ka aikata daga gare shi) misalin wannan alherin daga wancan, mafificin misalin shi ne fadinsa madaukaki: (zamu zo daga alheri daga gareta) da kuma fadinsa (kuyi azumi alheri ne gareku) anan wurin alheri yana iya kasancewa suna da ma'anar (aiki) ka aikata daga gare shi daga ciki akwai fadinsa madaukaki (ku yi guzuri hakika mafi alheri guzuri shi ne takawa) ma'ana ka aikata daga gare shi.

Shi alheri a wani lokaci yana kishiyantar sharri, a wani lokacin kuma kishiya ga cuta, misali fadinsa madaukaki:

 (وَإِن يَمْسَسْکَ اللّهُ بِضُرٍّ فَلاَ كَاشِفَ لَهُ إِلاَّ هُوَ وَإِن يَمْسَسْکَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدُيرٌ)

Idan Allah ya shafeka da cuta babu mai yayeta sais hi idan kuma ya shafeka da alheri hakika shi mai iko ne kan komai da komai.

Da fadinsa (cikinsu akwai mataye mafi alheri kyawawa) ance asalinsa ya zo da takfifi babu shadda sabida haka Kayyiran na nufin mataye mafi alheri, ana gaya namiji da mace wannan shi ne mafi alheri mazaje wannan matar itace zababbiyar cikin mata. Maganarsa ta zo karshe.