Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Kashe-kashen Takiyya a wurin Shaikul Ansari - HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Kashe-kashen Takiyya a wurin Shaikul Ansari

Babban Malaminmu Shaikul Ansari tareda tumbatsarsa cikin Fikhu da gogewarsa cikin fannin istinbadin hukunce-hukuncen shari'a na rassa daga dalilansa na filla-filla kadai ya gangara zuwa kashe-kashenTakiyya cikin Risalarsa daga mahangar Fikhun Ahlil-baiti Muhammad (s.a.w) ya zamana ya warware mas'alolin bisa la'akari da abinda ya rattabu kansu daga kebantattun hukunce-hukunce, yana farawa da karkasa su zuwa kashi biyu bayan ya kammala ta'rifinsu da bayaninsu a luggance da isdilahi, bisa la'akari da karkasuwar hukunce-hukunce taklifi guda biyar: wajabci, mustahabbi, haram, makaruhi, mubahi, da kuma hukunci wada'iyyu daga inganci da gurbata da dai abinda yayi kama da haka.

Yana cewa: (magana kan Takiyya a wani lokaci na kasance cikin hukunci taklifi a wani karon kuma cikin hukuncinta wada'iyyu) sannan ya rarrabata tareda la'akari da hukunci mwada'iyyu yana mai cewa: magana cikin na biyu a wani karon na kasancewa ta fuskar kufaifayin wada'iyyu da suka rattabu kan aikin mai sabawa gaskiya-daga inganci da rashinsa, a wani karon kuma cikin wadatarwa-lallai tana rattabuwa kan mai gangaro da takiyya kamar yanda take rattabuwa kan mai gangara bisa zabinsa haka take, ko kuma afkuwa aikin mai sabawa gaskiya bisa takiyya yana wajabta dauke wadancan kufaifayi, wannan duka a nahiya daya kenan amma a wata nahiya magana na kasancewa kan aiki mai sabawa gaskiya kamar misalin yin alwala kan koyarwa mazhabar da ta sabawa Ahlil-baiti shin kufaifayin gaskiya suna rattabuwa kansa daga inganci da wadatuwa da ita da rashin maimaita alwala ko ramata a halin takiyya ko kuma bta wadatarwa? Bari ya zama dole ne sharudda su cika su kammala kamar misalin rashin samun yalwar dama domin takiyya ta samu ingnata.

Sannan magana kan kufaifayin gaskiya na iya kasancewa iya cikin maimaice da ramuwa hakan na kasancewa ne idan aiki da ya gangaro da takiya ya kasance daga ayyukan ibada kamar misalin sallah, yana kuma iya kasancewa cikin wasu kufaifayin daba, lallai alwala da take kawar da hadasi wacce take halasta shiga ibada a mukamin gaskiya tana dauke hadasul asgar dangane da dukkanin salloli matukar dai bata warware, tambaya anan shin alwalar da akayi kan asasin takiyya shin tana dauke hadasi dangane da sauran salloli ko kuma dai ta takaitu da iya dauken hadasi da sallar da akeyi a mukamin takiyya? Haka zalika cikin mu'amalat shin mu'amalar da akayi kan asasin takiyya tana fa'idantar da kufaifayin ingancin mu'amala misalin mika kudi da karbar kaya?

Shaikul Ansari yana cewa: maganar tana kasancewa cikin mukamai hudu:

1-cikin hukuncinta na taklifi lallai ita takiyya tana karkasuwa ya zuwa hukunce-hukuncen taklifi guda biyar.

2-cikin rattabuwar kufaifayin gurbataccen aiki da ya kasance kan asasin takiyya nda rashin daukewar kufaifayi sakamakon takiyya.

3- cikin hukunci maimaici da ramuwa idan aikin da aka zo da shi a halin takiyya ya kasance daga ibada.

4-cikin rattabuwar kufaifayin inganci kan aikin da ya gangaro kan asasin takiyya bawaio ta fuskar kara'I da maimaici ba, babu banbanci cikin kasancewarsa daga ibada ne ko mu'amala.

Sannan cikin mukami na farko yana cewa: wajibi daga gareta shine wanda ya kasance domin tunkude cutuwar da ta zamana ta wajibi a take, misalsalan wannan suna da yawa.   

 

Mustahabbi: shine wanda ya kasance cikin akwai kauracewa da taka tsantsan daga fadawa cutuwa-ma'ana abinda zai jawo cutuwa ga mutum nan gaba, na farko na cikin wajibi shine cutuwar d atake yanzu gata a na ganin amma na mustahabbi itace wacce zata zo nan gaba, idan ya zamana kin aka tsantsan ko da kuwa kadan-kadan ne zai kwararar da mutum kan cutuwa kamar misalin kauracewa bi sannu-sannu tareda mutanen da suka sabawa mazhabar Ahlil-baiti da misalin kauracewa mu'amala da su cikin garuruwansu lallai galibin lokaci yin hakan na jawo yankewa da juna da gaba da kiyayya wanda suna haifar da mutum da cutuwa daga garesu cikin kankin kansa ko dukiyarsa  ko mutuncinsa.

Wannan yana daga nau'in takiyyar da Assayid Imam Komaini (ks) yake kiransa da takiyya bi sannu-sannu, sannan zahiri daga harshen yake kamar yanda zamu kawo kan cewa kwata-kwata bata kasance daga Takiyyar mustahabbi ba bari dai tama iya kasancewa ta wajibi a wasu wurare, saboda haka a lura sosai.

 

Mubahi: shine abinda ya kasance yinsa da barinsa su kasance kafada da juna bia daya daga mahangar shari'a, kamar misalin Takiyya cikin bayyana Kalmar kafi kan bayanin da wasu adadi daga Malamai sukayi ta iya yiwuwa wannan nau'i daga takiyya yana daga wanda ake kiransa da Takiyya Ikrahiyya wacce sassauci ya zo a kanta –hadisin Kissar mutane biyu da aka kama su a Kufa aka tilasta su zagin Sarkin Muminai (a.s) kan wannan nau'in takiyya hadisin yake bayani.

Sikatul Islami Kulaini ya rawaito da isnadi:

ثقة الإسـلام الشـيخ الكـليني بسـنده عن عبـد اللّه بن عطـاء قال : قلـت لأبـي جعفر 7:رجلان من أهل الكوفة اُخذا، فقيل لهما: ابرئا من أمير المؤمنين ، فبرىء واحد منهما وأبى الآخر، فخلّي سبيل الذي برىء، وقتل الآخر، فقال  : «أمّا الذي برىء فرجـلٌ فقيـه في دينـه وأمّا الذي لم يبرأ فرجـلٌ تعجّـل إلى الجنّة »[1] .

Sikatul islami Kulaini ya rawaito cikin isnadinsa daga Abdullahi Ibn Adda'u yace: na cewa Abu Jafar (a.s) mutane biyu daga mutanen garin Kufa an kamasu aka ce musu ko barranta kanku daga Sarkin Muminai, sai daya cikinsu ya barranata kansa dayan kuma yaki yarda da yayi, sai suka kyale wanda ya barranta kansa daga Sarkin Muminai (a.s) suka kashe wanda yaki yarda ya aikata hakan, sai yace: amma wanda ya barranta kansa daga Sarkin Muminai lallai shi mutum mai fahimta cikin addininsa amma wanda yaki yarda ya barranta kansa daga gareshi to lallai shi mutum da ya gaggauta shiga Aljanna.[1]

Makaruhi: shine wanda ya kasance barin takiyya da jurewa cutuwa da wahala yafi cancanta daga aikata ta ita takiyyar, kamar yanda wasu ba'arin Malamai suka ambaci hakan cikin bayyanar da Kalmar kafirci, lallai abinda yafi dacewa barin aikata hakan daga mutumi da ya kasance mutane suna koyi da shi-kamar misalin Malamai da mutane nagargaru domin daukaka Kalmar Allah. Abin nufi da makruhi a irin wannan lokaci shine wanda kishiyarsa yafi dacewa ma'ana dai makruhi da ma'ana A'ammi bawai wanda kebantaccen nassi ya zo a kansa ba, zahiri shine wannan magangara ita ma bata cika kan idlakinsa tama iya yiwuwa ta kasance daga haramtaciyya

Hakika hani da ya cikinsa hani na haramci bawai hani ne tanzihi ba (tsarkakewa) sai a lura sosai, nan gaba zamu yi bayani kan wannan gaba.

Muharram haramtacciyar takiyya: itace wadda take cikin jini lallai babu yin takiyya cikin jini kamar yanda ya zo cikin hadisai.

[1] Alkafi  juz 2 sh 175v hadisi mai lamba ta 21.