Mukaddima

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hasken sasannin cikin sanin arziki

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai tsananin karfi, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban mushugaban dukkanin annabawa da manzanni, Muhammad da iyalansa tsarkaka, musammam ma Bakiyatullahi cikin doran kasa wanda albarkacin sa dukkanin mutane al'ummu suke azurtuwa, da samuwarsa ne kasa da sama suka tabbatuwa, Allah ya gaggauta bayyanarsa.

Ya ubangiji ka bude bakina da Kalmar shiriya ka kimsa mini tsoranka.

Bayan haka: hakika wasu ba'arin matasa da suke cikin kishirwar sanin tabbatattun abubuwa da asrarun halitta da malakutiya, kuma masu binciken hakika da bayanin ma'arifofin muslunci musammam ma abin da ya zo daga kur'ani mai girma da madaukakiyar sunna hadisan manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka sun tambaye ni suka ce me ya sa muke rokon Allah yalwatar arziki, ko kuma muyi wasu wuridai da azkaru da salati da suka a hadisi don neman Karin arziki? Shin ba an rigaya an kaddara arzikin kowa ba, kuma duk wani jinjiri ana haifarsa tare da kaddararren arzikinsa kamar yanda aka kaddara masa rayuwa da mutuwa da arziki da tsiyata?

Amma kuma tare da haka sai muke rokon Allah ya yalwata mana arziki, tare da hakan mai wannan roko rayuwarsa bata gushe ba cikin kuntata da tsananta, kai kace talauci na bin sa a gindi ya sanya fikar sa kan ganagar jikin rayuwar sa, bari dai ta wani bangaren ma sai ka samu kafirin da kwata-kwata bai da addini ko kuma fasiki ko wawa gabo kasalalle Allah ya azurta shi da dukiya mai tarin yawa wacce zaka samu har mutane suna yi masa hassada?!

Yanzu wannan na daga adalcin ubangiji, ko kuma daga jabaru tilashi kamar yanda Ash'arawa suke rayawa?! Ko kuma daga rahamar Allah da hikimarsa ne?! shin haka na nufin kenan wanda bai yi wa kansa dabaibaiyi da dokokin addini ba yafi ni'imtuwa da samun farinciki daga wanin sa?!

A ina sirri al'amarin ya buya ne? menene labara na yakini? Da cewa Allah shi ne mai azurtawa ma'abocin karfi yana shimfida arziki ga bayinsa yana kuma kaddarawa, menene hikimar ubangiji wacce take tajalli cikin arzukan halittu da bayinsa?!

Amsata a wannan lokaci ta kasance takaitacciya, da cewa abin da yake wurin kafirai daga dukiyoyi baya nuni kyawuntar halinsu, bari al'amarin kishiyar hakan ne kamar yanda Allah matsarkaki ya fadi cikin littafinsa:

 (إنّما نُمْلي لَهُمْ لِيَزْدادُوا إثماً)[1]

Kadai dai mun jinkirta musu domin su kara daukan zunubi.

Wannan kau da kai da jinkiri daga dukiyoyinsu baya daga cikin ni'imar Allah, ba dukkanin dukiya bace take zama ni'ima, bari dai kudi da dukiya akwai masu kyau sune daga falala da ni'ima, hakan na kasancewa idan sun kasance daga Allah zuwa ga Allah cikin tafarkinsa, sannan daga dukiya akwai abar kyama wacce take daga azaba da daukar fansa, lallai shi yana daga sabubban aikata zunubi da sabo da laifuka da dagawa da zalunci.

 (كَلّا إِنَّ الاْنْسانَ لَيَطْغى * أَنْ رَآهُ اسْتَغْنى )[2]

Lallai mutum yana dagawa idan ya ga ya wadatu.

Kamar yanda Allah ya sanya rayuwar kafiari misalin rayuwar dabbobi bari dai tafi bata daga su, zukatansu kamar duwatsu bari sun fi duwatsu kekasa, sai Allah ya basu ya kuma azurta su kamar yanda yake azurta dabbobi. Amma maganarsa da kebantaccen ludufinsa da jin kai ya kebanta da muminai daga shi'ar sarkin muminai Ali bn Abu dalib (a.s) kamar yanda hakan ya tabbatu a muhallinsa.

Bayani filla-filla kan da yardar Allah- kadai dai abin da ake nufi daga arziki shi ne arzikin muminai maza da mata koma bayan kafirai maza da mata, sannan matsarkaki yana azurta wawaye kamar yanda ya zo cikin hadisai domin masu hankali suna fadaka da cewa shi arziki yana hannun Allah bawai wayon bawa da dabararsa ke bashi ba kamar yanda wasu ke tsammani.

Sannan maganar gaskiya cikin jabaru da tafwiz cikin abin da ya kebantu da ayyukan mutum kamar yanda Imam Sadik (a.s) ya fada:

«لا جبر ولا تفويض بل أمر بين أمرين »

Babu maganar jabaru haka babu maganar fawwalawa sai dai cewa al'amari ne tsakanin al'amura biyu.

 (وَأَنْ لَيْسَ لِلاْنْسانِ إِلّا ما  سَعى * وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرى )[5] .

Mutum bai da koma face abin da ya yi kai kawo kansa, kuma lallai da sannu za a ga sa'ayin sa.

Sannan shi arziki akwai wanda yake lamintacce kamar ci da sha wadanda kansu rayuwar gangar jiki ta dogara hakama cigaban rayuwar dabi'a har zuwa mutuwa

 (إِذا جاءَ أَجَلُهُمْ فَلا يَسْتَأْخِرُونَ ساعَةً وَلا يَسْتَقْدِمُونَ )[6]

Idan ajalinsu ya zo ba zasu su jinkirta dan lokaci ba kuma zasu gabace shi ba.

Wannan ne wanda Allah ya lamintar da shi ga dukkanin ma'abocin rai hatta daga tsirrai da dabbobi da mutane, lallai shi tun lokacin da ya zo duniya, Allah maida jini zazzakan nono tsarkakakke jinjiri ya dinga tsotsasa daga fatar nonon mahaifiyarsa ta hanyar ilhama da shiryarwa ta takwiniya daga ubangijinsa, kamar yanda Allah yanada arziki da aki kiran sa da rizkul maksum da kuma mamluk da mau'ud.

Bayanin hakan: sai muce cikin amsa filla-filla: lallai Allah ya lamintar da arzki na farko-farko ga dukkanin ma'abocin rai, sai dai cewa cikin domin karrama shi kan sauran halittu 

 (وَلَقَدْ كَرَّمنا بَني آدَمَ )[7]  

Hakika mun karrama `dan Adam.

Domin daukakarsa da ilimi da zabi da yanci da taklifi a jumlace, da jarraba shi domin ya san mummuna daga kyakkyawa ya san banbace karya da gaskiya, domin sanin mai `da da mai sabo.

 (الَّذي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَياةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً)[8]

Shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku wanene cikinku yafi kyawunta aiki.

Hakika ya karkasa arziki tsakanin bayi da hikima da adalci, wannan shi ne abin da ake kira da rababben arziki (Arrizkul maksum) yana daga kaso na biyu daga arziki, sannan shi adalci ubangiji baya nufin daidaito cikin kaso, bari dai shi adalci na nufin ajiye komai a muhallinsa, sai ya azurta wanda ya so ya shimfida arziki ga wanda ya so ya kuma kuntatawa wanda ya so da abin da hikimarsa take hukuntawa, daga cikin bayi akwai wanda ya kasance mawadaci akwai kuma talaka, ya sanya kowanne dayansu wazifofi da nauyi, talauci da wadata ba komai bane face jarrabawa, domin ya san wanene cikinsu yafi kyawunta aiki, shin mawadaci cikin sauke hakkokinsa, ko kuma talaka cikin hakuri da juriya, ya jarraba mawadaci da wadata, ya umarce shi da sauke hakkokin dukiyarsa, lallai cikin dukiyarsa akwai hakkin mai roko da haramtacce daga dukiya, lallai shi wakilin Allah ne cikin iyalinsa, hakama ya jarrabci talaka da talauci, ya umarce shi da yin hakuri da juriya da kana'a, wannan ibtila'i yana daga sunnonin Allah kuma babu sauyi cikin sunnoninsa, lallai tana daga tabbatattun abubuwa na halitta, tana kuma gudana cikin dukkanin kishiyoyin juna, kamar rayuwa da mutuwa, lafiya da ciwo, izza da zilla, kuntata da yalwata, da abin da ya yi kama da haka.