lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kibiya ta shida

 

Gina Kaburburan Salihan bayin Allah da ziyartarsu

Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yana cewa:

«العالم بزمانه لا تهجم عليه اللوابس »                            

Malami masanin zamininsa shubuhohi basa rikita shi.

Lallai shi yana kallo da duba da hasken Allah matsarkaki kamar yanda ya san hukunce-hukuncen Allah matsarkaki sai Allah ya wurga ilimi cikin zuciyarsa ya nuna masa tabbatattun abbubuwa ya haska masa sirrikan al'amura kamar yanda yake riskar boyayyunsu, yana sanin zamaninsa da ma'abota zamaninsa gaskiya ba ta jirkice masa da karya haka karya ma ba ta jirkita da gaskiya a wurinsa, bari dia shi sarai yana sanin Munafuki daga furucinsa da yanda yake aikinsa.

Hakika Mumini Masanin zamaninsa yana sanin cewa Shaidanu suna wahayi zuwa ga Masoyansu kamar yanda Allah ya bada labarin hakan, daga Masoyan Shaidan lokaci zuwa lokaci zaka samu bidi'o'i da shubuhohi da kagaggun abubuwa suna bayyana, zaka same su suna kira zuwa ga sabuwar hanya da kirkirarriyar Mazhaba wacce a zahirinta muslunci da tauhidi, amma badininta kafirci da munafunci kamar misalin da'awar Baha'iyya da Babiyya da suke tsakankanin `yan shi'a, hakan zalika da'awar Wahabiyya cikin Ahlus-sunna a wannan zaman- daga cikin al'adarsu karya da kage kan gaskiya da kokari da kai kawo domin rusa hasken addini da dogon gininsa, sai dai cewa sun makara Allah yaki yarda da burinsa sai ya cika haskensa ko da kuwa Musrikai da Kafirai basa son hakan.

Bidi'ar Wahabiyya ta bayyana a karni na 20 daga garin Najad wanda daga nan Kahon Shaidan zai huda, sune mabiyan Muhammad bn Abdul-Wahab Annajadi.

An haife shin a garin Uyainatu cikin Najad a shekara 1115 Kamariya, babansa ya kasance Alkali, ya karanta fikhul Hanbali a wurin babansa, sannan yayi tafiya zuwa Madina daga nan ya tafi garin Basara dana ya tafi garin Sham daga nan ya tsallaka garin Ahsa'u…. a cikin shekara ta 1139 hijiri ya raka mahaifinsa cikin tafiye-tafiyensa sannan yayi jayayya da shi cikin Akidun mutane har lokacin da ya bar duniya a shekara 1153 hijiri, Usman bn Hammad shugaban garin Uyainatu ya biyewa Muhammad bn Abdul-Wahab cikin karkatattun akidunsa al'amaarin da ya kai ga korarsa daga garin a shekara ta 1160 ya koma Addar'iya daya daga garuruwan Najad sai Sarkin garin Muhammad bn Sa'ud wanda shine kakan Sa'ud ya karbe shi.

Muhammad bn Abdul-Wahab yana ganin cewa duk wanda bai yi imani da Akidunsa ba Kafiri Mushriki kuma ya halasta a kai masa hari a kashe shi a kwace dukiyarsa da bautar da iyalinsa, da wannan hare-hare lokaci zuwa lokaci ya fara daga bangaren Alu Sa'ud da Jahilan Mataimakansu mayunwata `yan hayaniya suka dinga yakar garruruwa da suke makotansu, Muhammad bn Abdul-Wahab ya mutu a shekara ta 1206 sai dai cewa Mazhabarsa ta cigaba da yaduwa tsakankanin dangin Sa'ud, daga cikin takensu akwai rusa Kubbobin Kaburburan Waliyyai da Salihai da sace dukiyar d atake ajiye cikin harami mai daraja a fadin duniya cikin dukkanin wajen ziyara, daga wannan akida ne suka kai hari kan Karbala Mu'alla suka kashe rayukan da basu da laifi daga mata da kananan yara  suka sace dukiyoyin mutane, duka hakan ya faru ne a shekara ta 1216 cikin rundunar sojojinsu da ta kunshi mayaka dubu ashirin.

Amma Akidun da Wahabiyyawa suka dayantu da su koma bayan dukkanin musulmi da Mazhabobinsu da kungiyoyinsu  daga Sunna da Shi'a, lallai zamu Ambato wasu adadi daga cikinsu tareda yin raddi kansu da takaitacciyar munakasha domin ya zama mafara ga wanda yake son zurfafa bincike, sannan mu tantance tareda sanin gaskiya da ma'abotanta.

Wahabiyyawa cikin tauhidi suna raya cewa Allah yana da gangar jiki amma fa ba kamara sauran gangar jikkuna ba, lallai yana wani bigire da kusurwa kuma yana da gabobi da sassan gangar jiki kuma yana gani da idanu dukkanin wannan maganganu sun biyewa babban Malaminsu Ibn Taimiyya wanda ya mutu a shekara 728 da hijira kuma kan haka dalibinsa Ibn Kayyum Jauziyya ya tafi, suna masu cewa: Allah yana saukowa daga Al'arshinsa zuwa sama ta daya kamar misalin yanda mai huduba yake saukowa daga kan Minbari, babbar masifa shine Wahabiyyawa bisa imani da wannan gurbatacciyar akida suna raya cewa suna ma'abota riko da tacaccen tauhidi kuma kungiyarsu itace take kan tsira sannan sauran kungiyoyin musulmai dukkaninsu suna wuta!!

Kuma suna raya cewa yin tawassuli da Annabi (S.A.W) da Waliyyai haramun ne, da wadannan busassun akidu na rashin imani da wayewa da tsabar gidadancinsu suke son nuna muslunci da bayyana yanda yake ga duniya, sai dia cewa duk mutumin da yake bibiyar wadannan karkatattun tunanunnukansu da sannu zai gane cewa wannan mazhaba ta sub a zai taba yiwuwa ta hidimtawa muslunci ba da amfanar da shi a matsayinsa na addini daga Allah da yake dacewa da dukkanin zamani da kasashe.

Mutum na farko d aya fara sabawa Muhammad bn Abdul-Wahab cikin karkatattun akidunsa shine `dan'uwansa Sulaiman bn Abdul-Wahab cikin littafinsa (Assawa'ikil Ilahiyya fi Raddi ala Wahabiyya).

Bayan hare-hare na rashin kan gado Haramin Makka da Madina ys fada hannun Wahabbiya hakan ya faru ne karkashin makirci da taimakon Turawan mulkin mallakar Birtaniya baya rushewar babbar Daular Usmaniyya.

Farkon wanda ya fara sukan Wahabiyyawa daga Malaman muslunci daga bangaresn shi'a da ya tona asirinsu da bacewarsu shine Almuhakkikul A'azam Shaik Jafar Kashiful Gida wanda ya bar duniya shekara 1228 hijiri, ya bayyana hakan ne cikin littafinsa (Minhajul Rashad.

Hakika Ibn Taimiyya cikin littafinsa Zadul Ma'ad fi Huda Kairul Ibad, yayi fatawar rushe Kaburbura, lokacin da Alu Sa'ud suka samu mulki suka kwace Madina da Makka a shekara 1334 sun rusa Kaburburan da yake cikin garuruwan daga cikinsu akwai Kaburburan A'immatul Baki'a da kaburburan Salihai cikin wannan mummunan aiki suna jingina da hadisin Abi Hayyaj daga Sarkin Muminai Ali (A.S) da cewa shi ya daidaita kauburbura. A daidai wannan lokaci suna kafa hujja kan halascin gine-ginen Kaburbura da dogwayen gidajensu bari ma harda mustahabbancin raya su da daga gininsu da fakewa da dalilai hudu daga littafin Allah da ayoyinsa kamar fadinsa madaukaki:

(ومن يعظّم شعائر الله فإنّها من تقوى القلوب )

Kuma duk wanda ya raya hukunce-hukuncen Allah lallai hakan na daga takawar zukata.

Sha'airi suna daukar ma'anar Alamomi, alomomin addinin Allah kamar misalin dutsen Safa da Marwa, da waliyyan Allah da Salihai daga Malamai duka suna daga Sha'a'ir din Allah, girmama kaburburansu da karramasu na daga girmama Alaman Allah, idan hadaya da dabbar yanka daga Rakumi- a kwanakin aikin Hajji lokacin sanya musu alama da saisaye su ba a hawansu sabida girmama alamin Allah, to yaya kaburburan Shahidai da Malamai da Salihai da asiyyai da Annabawa?! Yanzu sai ya zamana kenan kuna rusa su, sannan ga fadin Allah ta'ala:

 (قل لا أسألكم عليه أجرآ إلّا المودّة في القربى )

Kace ni bana tambayarku wani lada face nuna soyayya cikin makusanta.

Daga cikin soyayya da tarsashin haskenta akwai girmamawa da gina kaburburan Annabawa da Wasiyyai.

Da fadin Allah cikin kissar As'habul Kahafi:

 (ابنوا عليهم بنيانآ)

Ku gina wani gini a kansu.

Lallai gini yana daga girmamawa da karramawa da tsarkakewa ga As'habul Kahafi.

 (وقال الذين غلبوا على أمرهم لنتّخذن عليهم مسجدآ)

Kuma wadanda suka yi galaba kan lamarinsu suka ce tabbas zamu riki gini kansu.

Sannan duk abinda Kur'ani ya tabbata hujja ne, Kur'ani baiyi inkarin abinda aka aikata daga gini cikin As'habul Kahafi ba da masallaci.

Sannan fadinsa ta'ala:

: (الله نور السماوات والأرض )

Allah shine hasken sammai da kasa.

Kamanta wannan haske da haske mai huda cikin Alkurkinsa mai Albarka kuma shi yana cikin wasu gidaje Allah yayi izini a dagasu a ambaci sunansa ciki, ya zama tilas a daukaka daraja da matsayin wadannan gidaje na Allah kadai dai dagasu zai kasance ta hannun Muminai mazansu da mata, wadannan gidaje basu takaitu da iya masallatai ba bari dai ta hada da gidajen Annabawa, gidan Ali da Fatima na daga mafi falalarsu kamar yanda ya zo daga riwayoyin shi'a da sunna cikin karshen ayatun Nur- sannan shi gida shine abinda cikinsa akwai rufi, daidai lokacin da mustahabbi ne ga masallatai ka da a yi musu rufi, sannan dagawa ya fadadu daga dagawa ta zahiri kamar dai fadinsa ta'ala:

 (إذ يرفع ابراهيم القواعد من البيت )

Yayinda Ibrahim yake daga harsashin gini daga gida.

Wannan aya tana daga dagawa ta badini, sabida haka cikin kowanne hali wajibi a daga gidajen Waliyyai a lokacin da suke a raye da bayan mutuwarsu.

Tareda wannan ayoyi masu daraja da misalsalansu ta yaya zai halasta ga Wahabiyawa su rusa gidajen da ake ambaton sunan Allah?!

Musulmai a farkon muslunci lokacin bude garuruwa basu rushe kaburburan Annabawa ba, bari dai tsawon karnoni da suka zo daga baya duk babu batun rushesu bari ma dai an ginasu neda mikar da katangunsu, kamar yanda musulmai suka al'adantu da kai musu ziyara, samuwar misalin wadannan gine-gine da suka zama ramzin muslunci da musulmai cikin duniya a gaban idanun malamai da kunnuwansu tsawon karnoni da suka gabata dallili ne mabayyani kan ingancin aiki da rinjayarsa, da rashin haramcin gina kabari.

Sannan bada kariya kan kaburbura da kula da su cikin yin hakan akwai fa'idoji na badini masu tarin yawa, hakika Almasihu bn Maryam a gurin Turawan yamma ya kusa wayar gari tatsuniya sakamakon rashin kufaifayi da suke nuni zuwa gareshi, sabanin Annabin muslunci shi yana da kufaifayi da suke shirywarwa zuwa ga samuwarsa da hakikarsa, kan misalin wannan ne musulmai suka himmatu cikin tabbatar da tarihin Annabi da kufaifayinsa hatta rijiyar da yayi tofi cikinta ko kuma wacce zobensa ya fada cikinta.

Cikin dukkanin garuruwa da kasashen musulmai ana bada kulawa kan kufaifayin Waliyyai da Salihai daga cikinsu kaburburansu tsarkaka wadanda suka kasance masaukar Mala'iku kuma suna daga wuraren da ake karbar addu'a da saukar albarkoki.

Cikin kowanne zamani musulmai sun kasance su himmatuwa matuka cikin sabunta ginin Kabarin Annabi Muhammad (S.A.W) domin sanin hakan kana iya duba littafi Malam Samhudi mai suna (Wafa'ul Wafa).

Amma hadisai:

قال عليّ  7 لأبي الهياج : ألا أبعثُکَ على ما بعثني عليه رسول الله  9، أن
لا تدع تمثالا إلّا طمسته ولا قبرآ مشرفآ إلّا سوّيته .

Ali amincin Allah ya tabata a gareshi ya cewa Abu Hayyaj: yanzu bana turaka kan abinda Manzon Allah (S.A.W) ya tura ni kansa ba, Kada ka bar wani Gunki face ka ruguje shih aka kada ka bar wani dogon kabari face ka daidaita shi.

Dogon kabari shine wanda aka mikar da shi kamar tozon Rakumi, sannan daidaitawa bata nufin rusa shi kamar yand aWahabiyyawa suka fassara da gubatattun akiduns, da daidaitawa na nufin rusawa to me yasa Malamai basu yi fatata kan hakan ba, kamar yanda Mazhabobi suke rinjayar da mikar da kabari gwagwadon tsayin fadinh tafin hannu.

Sabida haka ma'anar (sawwaitahu) shine ka sanya shi kwance samansa ya daidaita da kusurwowinsa bawai kamar tozon Rakumi ba wanda ya kasance daga alamomin Yahudu.

Mai sharhin littafin Sahihu Muslim cikin bayanin riwayar yana cewa: hakika abinda yake a sunna shine kada a mikar da tsayin kabari yayi yawa kuma kada ya zama da yanayin tozan Rakumi, bari dai za a dagashi mikdarn fadin tafin hannu sannan ya zamana shimfide.

Sannan da abinda ake nufi da daidaita kabari shine rusa shi to me ysa shi kansa Sarkin Muminai (A.S) bai rusa ba me ya bai ruguje Kubbobin da suka kasance a zamaninsa ba.

Kaddara ma mun sallama ingancin hadisin da cikar ma'anarsa, lallai kololuwar abinda yake kunshe cikinsa shine daidaita kabari da kasa, lallai baya shiryarwa zuwa ga rusa gini da kubbobi da suke kewaye da kabarin, sabida dai bai ce kada ka bar wani gini ko kubba face ka daidaita su.

Sannan akwai tsammanin cewa Sarkin Muminai (A.S) yayi umarni da daidaita kabari sakamakon riko da shi alkibla da masallaci, wannan kuma bai da wata alaka da kaburburan musulmai, sannan abinda daga surori shine Gumakai sannan kaburburan da yake nufi sune kaburburan Mushrikai, kadai Fakihai hudu sun yi ittifaki ne kan makaruhancin gina gida kan kabari bawai wancan haramci da wahabiyawa sukai da'awa ba.

Amma kafa hujja da dalili da hadisin Jabir da aka nakalto daga Bn Jarihu da Abu Zaidu to wannan hadisai dai ra'ifi ne.

عن جابر قال : نهى رسول الله أن يجصّص القبر وأن يقعد عليه وأن يبنى عليه.

An karbo daga Jabir yace: Manzon Allah (S.A.W) ya hana simince  Kabari hakama tsugunawa a kansa da gina shi.

Sai dai cewa matanin wannan hadisai ya samu raurawa lallai an nakalto da kalmomi bakwai wanda hakan yana shiryarwa kan raurawar matanin, idna ma mun kau da kai daga isnadin da dalalarsa, tofa lallai harafin wawun da yake hade da hani baya shiryarwa kan haramci bari dai yana daga hani na tsarkakewa (Nahayul tanzihi) kamare yanda ya kunshi hani kan zama kan kabari wand aba haramun bane bari dai hani ne na tsarkakewa wanda yake da ma'anar makaruhanci, sai ya zama kenan makaruhi ne gini kan kabari, sannan wannan baya cin karo da Unwanul Sanawi da yake shiryarwa kan rinjaya da mustahabbanci kamar misali domin kiyaye kufaifayin muslunci da girmama Alamomin Allah.

Haka magana cikin hadisin Abdur-Rahman bn Yazid daga Jabir daga Kasim bn Mukaimaratu daga Abu Sa'id:

إنّ النبيّ  9 نهى أن يبنى على القبر.

Lallai Annabi (S.A.W) ya hana gini kan Kabari.

Sannan da gini kan kabari haramun ne, lallai kasance daga la'akari daga sabunta gini, sabida haka to me yasa Wahabiyawa suka rushe abind aya kasance daga asalin ginin, da ace an haramta sabuntawa da wanzarwa to me yasa aka binne Annabi (S.A.W) cikin gini kuma har wannan lokaci yana nan cikin ginannen waje.

Wahabiyawa cikin akidunsu na bata da batarwa sun sabawa musulmai da Malaman fikhunsu da abind aake aikatawa daga neman tabarruki da tsarkakakkun kufaifayu da girmama alaman ubangiji.

Amma fadin cewa filin Makabartar Baki'a wakafi ne kamar yanda Wahabiyawa suke da'awa lallai wannan yana daga abinda babu dalili kansa, kasa dai tana nan kan halascinta na fari, farkon wanda aka fara binnewa a Baki'a shine Sahabin Annabi (S.A.W) Usmanu Bn Maz'un Allah ya kara masa yarda, lallai Annabi (S.A.W) da sahabbansa sun kasance suna ziyartar mutanen da suke kwance a makabartar Baki'a.

Wannan kenan sannan mun kawo wannan bayani daga ka'idar (Alzimuhum bima Iltizamu bihi) mun kafa musu hujja da litattafansu, amma litattafanmu da riwayoyin malamanmu lallai akwai tarin dalilai da suke shiryarwa kan mustahabbanci raya kaburburan Annabawa da Wasiyyai da Salihai da ziyartarsu da hallara cikinsu.

Tura tambaya