lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kada ka cutar da wanda kake baiwa Sadaka


Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai
 
Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka. 

Bayan haka:
B yi godiya ga Allah da kuma wanda ya baiwar domin ta hanyarsa ne ya samu damar zama sila da tsanin kwararar Failolin da ni'imomin ubangiji zuwa ga bawansa. 
Haka zalika Mai Mai karɓa shima ya zama dole ya mutunta mai bashi ganin ya zaɓe shi  zama muhallin taimakonsa.
Ƙur'ani Mai girma ya yi tsawatarwa kan haka cikin ayoyi da daman gaske ta yiwu mafi zama da bayyanuwa matsayin misdaƙin wannan ma'ana itace aya mai daraja cikin faɗinsa madaukaki:

(قَوۡلࣱ مَّعۡرُوفࣱ وَمَغۡفِرَةٌ خَیۡرࣱ مِّن صَدَقَةࣲ یَتۡبَعُهَاۤ أَذࣰىۗ وَٱللَّهُ غَنِیٌّ حَلِیمࣱ)
kyakkyawan zance da gafara yafi zama mafi alheri daga Sadaƙar da cutarwa ke biyo bayanta kuma Allah Mawadaci ne Mai Haƙuri
[Surah Al-Baqarah 263]

Ma'aruf: duk wani abu da hankali da shari'a suke Itirafi da shi kishiyan Munkari.

bugu da ƙari ciki aya da take kusa wacce ta gabata tsawatarwa ta zo kan hakan:

(یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ لَا تُبۡطِلُوا۟ صَدَقَـٰتِكُم بِٱلۡمَنِّ وَٱلۡأَذَىٰ 
[Surah Al-Baqarah 264]

Yaku waɗanda suka yi imani ka da ku gurɓata Sadaƙoƙinku da gori da cutarwa.

Haƙiƙa kan wannan ma'ana hadisi ya zo daga Annabi (s.a.w):

إذا سألك سائل فلاتقطعوا عليه مسألته حتى يفرغ منها، ثم ردوا عليه بوقار ولين، إما ببذل يسير، أو رد جميل، فقد يأتيكم من ليس بإنس ولا جان، ينظرون كيف صنيعكم فيما خولكم الله تعالى.

Idan Almajiri ya roƙeka ka da ku yanke masa magana ku hana shi bayanin bukatar da ta kawo shi ku jira har ya gama bayani, sannan ku bashi amsa cikin girmamawa da lausasawa, ko da bashi ɗan abinda ya samu, ko kuma bashi hakuri da kyawawan kalamai, haƙiƙa ta yiwu wanda ba mutum kuma ba Aljani ba ya zo muku domin domin ganin yanda kuke tasarrufi cikin abinda Allah ya ni'imtaku da shi.

Umar Alasan
Faroukumar66@gmail.com 

Tura tambaya