lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Albarkacin wahalar wasu



da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai

Dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin talikai tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Hakika tsarin rayuwa yana hukunta kowanne bil Adama ya kasance yana da wata gudummawa da yake bayarwa domin samun daidaituwar system ɗin duniyar asbab.
cikin hakan rayuwa ta hukunta samun wasu ma'abota himma da zasu jiɓanci samarwa al'umma abinci, wasu kuma su ɗauki nauyin samar da nama da madarar sha, wasu kuma su jibanci yin karatun lafiya domin samar da likitoci wasu Engineering, wasu kuma aikinsu shine tsayar da adalci da datse hannun duk wani ɗan ta'adda, dss
wannan shine sunnar rayuwa kuma sunnar Allah
ولن تجد لسنة الله تبديلا.
babu sauyi cikin sunnar Allah.
Kuma wannan shine tsarin da duniyar asbab ta ɗoru akai.

Imam Assaɗik (a.s)
أبى الله أن يجري الأمور إلا بأسبابها.
Allah yaƙi yarda ya gudanar al'amura sai tareda sabubbansu.

wannan sunna ta hukunta wasu su sha wahala albarkacin wannan wahalar wasu kuma su huta.
daga mafi bayyanar ayar Ƙur'ani Mai girma da ta ƙunshi wannan itace wannan ayar
ولولا دفع الله الناس بعضهم ببعض لفسدت الارض.
ba da ban Allah ya tunkude mutane sashensu da sashe da ƙasa ta gurbace.

Da system ɗin ya samu matsala.
Sannan ƙarƙashin wannan ayar ne hadisi daga Manzon Allah (s. a.w):
إن الله يدفع العذاب بمن يصلي عمن لا يصلي. بمن يزكي عمن لايزكي. بمن يصوم عمن لا يصوم. بمن يحج عمن لا يحج. بمن يجاهد عمن لا يجاهد. لو اجتمعوا على ترك هذه الأشياء من أنظرهم الله طرفة عين. 
Haƙiƙa Allah yana tunkuɗe azaba albarkacin wanda yake sallah daga wanda ba ya yi, albarkacin wanda yake bada zakka daga wanda baya bayarwa. albarkacin wanda yake azumi daga wanda ba ya yi. albarkacin wanda yaje Hajji daga wanda baya zuwa, albarkacin wanda yaje jihadi daga wanda baya zuwa, da dukkaninsu zasu haɗu kan watsi da waɗannnan ayyuka da Allah bai ɗaga musu ƙafa ba gwargwadon kiftawar ido. 
Umar Alhassan Salihu
Faroukumar66@gmail.com

Tura tambaya