lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU – BAHASI KAN DAGATAWA DA TSAYAWA KAN GABOBIN AYOYI


Wuri: birnin Qum mai tsarki- MUNTADA Jabalu Amil Islami-tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi (H)

Lokaci: karfe 8 zuwa 9 na Safiya.

Fikhu (86) 24 ga watan Jimada thani shekara 1441Q.

Muhakkikul Hilli Allah tsarkake sirrinsa yana cewa: na biyar shine wakafi kan gabobin ayoyi.

Daga cikin mustahabban kira'a shine tsayuwa da dagatawa kkan gabar kowacce aya kamar yanda Mash'hur suka zabi wannan ra'ayi, da farko dai abinda aka nakalto daga Majma'u cikin wani hadisi mursali yana shiryarwa kan wannan ra'ayi, sannan raunana da hadisi yake da ita tana warwarewa sakamakon Malamai sunyi aiki da wannan hadisi:

عن أم سلمة قالت: (كان النبي صلى الله عليه وآله وسلم يقطع قراءته آية آية) ([1]).

An karbo daga Ummus Salama tace: Annabi (s.a.w) yana daddatsa kira'arsa daki daki aya zuwa aya.

Fuskar kafa dalili: a bayyane yake hakika daddatsa kira'a aya zuwa aya yana da ma'anar wakafi da tsayuwa kan gabobi, tabbas kuna da abin koyi mai kyawu cikin Manzon Allah, lallai zancensa daidai yake da aikinsa daga sunna yake.

Na biyu: abinda ya gabata cikin ma'ana da tafsirin Rutaili kamar yanda ya zo cikin littafin Alwafi daga Faizul Kashani  hakama cikin Majma'ul Bahraini an danganta wannan magana zuwa ga Sarkin Muminai Ali (a.s)  bayan danganta ta ga Annabi (s.a.w) cewa shi : (ya kiyaye wakafi da furta haruffa) bisa gini kan cewa abinda ake nufi daga wakafi shine tsayuwa kan gaba da karshen kowacce aya da ma'ana yin gajeren shiru bawai kawai jinkiri da kauracewa yin gaggawa ba kadai kamar yanda bayani ya gabata.

Sai dai kuma tareda hakan anyi ishkali kansa: akwai yiwuwa daukar fuskar ma'ana biyu cikin wakafi daga abinda yake jawo dunkulewa cikin maganar sai ya zama hadisin ya fadi daga kafa hujja da shi sai dai idan an zabi cewa ma'anar da ake so bata bayyana karara ba kadai bayani ne kan yankewa bisa dogaro da abinda zauki ke gani kyawunsa tareda kallon ma'anar magana da kuma sallama hakan zuwa ga mahangar mai karatu, a cikin shifci da rubutun ka'idojin rubutu na zamani a yau kadai dai a na sanya wakafi a matsayin gaba da madagakata cikin zance tareda la'akarin mai karatu da tukewar numfashi, daga nan kuma tana iya yiwuwa wani ya fadada wani kuma ya tsuke domin lamarin ya dogara ne da zauki cikin sirrin kira'a, sai ka lura, hakika tantancewa hakan yana komawa zuwa ga Urfi al'ada.

Ita ko al'ada kamar yanda ake fadi (tana bakin kofarka, daga karshe ra'ayin da muka zaba shine abinda Muhakkikul Hilli Allah ya tsarkake sirrinsa ya tafi kansa.

Na shida: (kallon ma'anar abinda ake karantawa da kuma wa'aztuwa da su).

Ina cewa: wannan mustahabbi ne na shida daga cikin mustahabban kira'a, lallai yana daga abinda aka rinjayar wanda kuma ake samun lada kansa a wasu ba'arori sakamakon samuwar maslaha wacce take bata larura ba lallai yayin kira'ar Fatiha da sura ana son mai karatu yayi tadabburi cikin ayoyi da ma'anar da suka kunsa da mafahim dinsu kuma ya wa'aztu da su, lallai Allah matsarkaki ya umarci Annabinsa da ya kira mutane ya zuwa tafarkin ubangijinsa da hikima da kafa hujja ga ma'abota hankula da basira misalin malamai da masana hikima kuma cikin kiran yayi amfani da wa'azi mai kyawu ga musulmai da muminai bai daya ya kuma yi ja'in ja da masu kishiyantarsa  misalin Ahlil kitabi daga Yahudawa da Nasara da wasunsu daga mushrikai da mafi kyawu.

Shi kur'ani mai girma shiriya ne ga baki dayan mutane haka kuma a kebance shiriya ne ga masu tak'wa kamar yanda ya kasance wa'azi da farinciki duniya da lahira, sabida haka abind aya fi kamata mai sallah mai karanta kur'ani babu banbanci namiji ne ko kuma mace da suyi tadabburi su wa'aztu da bayanan Allah madaukaki matsarkaki.

Ya zo cikin littafin Alwasa'il babi na uku daga cikin abwabul kira'atul kur'an cikinsa akwai riwayoyi guda takwas taken babi shine: Babul istihbabil Attafakur fil ma'anil Kura'ni wa amsalii wa wa'adihi wa wa'idihi ya zuwa karshe.

A riwaya ta bakwai: cikin (Ma'ani Akbar) sh 67   

عن أبيه عن محمد بن القاسم عن محمد بن عليّ الكوفي عن محمد بن خالد عن بعض رجاله من واد والرّقي عن أبي حمزة الثمالي عن أبي جعفر عليه السلام قال: قال أمير المؤمنين عليه السلام.

ألا أُخبركم بالفقيه حقّاً؟ من لم يقنط الناس من رحمة الله، ولم يؤمنهم من عذاب الله ولم يؤيهم من روح الله، ولم يرخّص في معاصي الله، ولم يترك القرآن رغبة عنه إلى غيره، ألا لا خير في علم ليس فيه تفهّمالا لا خير في قراءة ليس فيها تدبّر، إلّا لا خير في عبادة ليس فيها تفقّه.

Daga babansa daga Muhammad Ibn Kasim daga Muhammad Ibn Aliyu Alkufi daga Muhammad Ibn Kalid daga ba'arin wasu mutanensa daga Waddul Arriki daga Abu Hamzatul Assimalidaga Abu Jafar amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce: Sarkin muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce: yanzu bana baku labari da hakikanin Fakihi ba? Shine wanda baya debewa mutane tsammani daga rahamar Allah, shine wanda baya amintar da su daga azabar Allah bai nesanta su daga ni'imar Allah, bai kuma saukaka musu sabon Allah, bai barin kur'ani sabida kyamarsa ya zuwa ga waninsa, ku sani babu alheri cikin ilimin d acikinsa babu fahimta  babu alheri cikin kira'ar da cikinta babu tadabburi, babu alheri cikin ibadar da ba ta kunshe da fahimta.

ورواه الكليني عن عدة من أصحابنا عن أحمد بن محمد البرقي عن إسماعيل بن مهران عن أبي سعيد القماط عن الحلبي عن أبي عبد الله عليه السلام قال: قال أمير المؤمنين عليه السلام وذكر الحديث نحوه.

Kulaini ya rawaito daga wasu adadi daga malamanmu daga Ahmad Ibn Muhammad Albaraki daga Isma'il Ibn Mihran daga Abi Sa'id Alkammad daga Halabi daga Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya ce: Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi ya fada ya kuma ambaci wani hadisi makamancinsa.

وفي الرواية السادسة: في (المجالس: ص: 341)  عن محمد بن الحسن عن الصفار عن علي بن حسّان عن أمير المؤمنين عليه السلام في كلام طويل في وصف المتقين قال: أمّا الليل فصافّون أقدامهم تالين لأجزاء القرآن  المؤمنين عليه السلام في كلام طويل في وصف المتقين قال: أمّا الليل فصافّون أقدامهم تالين لأجزاء القرآن يرتلونه ترتيلاً، يُحزنون به أنفسهم، ويستثيرون به تهيج أقرانهم، بكاء على ذنوبهم ، ووجع كلوم جراحهم، وإذا مرّوا بآية فيها تخويف أصغوا إليها مسامع قلوبهم وأبصارهم، فأقشعرت عنها جلودهم، ووجلت قلوبهم، فظنوا أنّ صهيل جهنّم وزفيرها وشهيقها في أصول آذانهم، وإذا مرّوا بآية فيها تشويق ركنوا إليها طمعاً، وتطلعت أنفسهم إليها شوقاً، وظنوا أنها نصب أعينهم.

 Ya zo cikin riwaya ta shida cikin Majalis sh:341 daga Muhammad Ibn Hassan daga Saffar daga Aliyu Ibn Hassan daga Sarkin Muminai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi  cikn wata doguwar magana  cikin siffanta masu tak'wa ya ce: amma da daddare zaka samu sun mikar da kafafunsu  suna tilawar kur'ani  suna karanta shi suna jeranta shi jerantawa, suna bakantawa rayukansu da shi, suna fifita da shi daga motsin tsaraikunsu, suna masu kuka kan zunuban da suka aikata, da radadin ciwukan, idan suka wuce wata ayawacce cikin akwai tsoratarwa su jingina kunnuwan zukatansu da basirasu sai fatar jikunsu ta kwansare zukatansu su razana su tsorata, sai suji cewa kamar karajin jahannama da karar zababbakarta na kugi cikin kunnuwansu, idan suka gifta wata aya da take kwadaitarwa sai karkata gareta sabida son ya rai da tsammani, rayukansu su dinga tsinkaya zuwa kanta sabida shauki su ji cewa ta kasance rabo ga idanuwansu.

Abinda wannan hadisi ya kunsa bai buy aba hakama abinda yake nuni zuwa gareshi daga girmamar kur'ani mai girma daga gwala-gwalan ma'anoni madaukaka da mafahim masu daukaka da daukakarsa madaukaki mafi daukaka jalla jalaluhu, ta yaya hakan ba zai kasance ba alhalin shi kur'ani zancen Allah n Azza wa jalla, zahirin nada kyawu badininsa kuwa na da zurfafa, cikinsa mahaskakar shiriya take cikinsa fitilun haskake duhu, mai neman yaye duhu daga idonsa yana yayeshi da kur'ani, yana bude basirarsa da haskensa, hakika tunani rayuwa ce zuciya mai gani kamar yanda yake tafiya yana mai haskaka cikin duhu da haskensa, idan fitintinu suka rudar da ku kamar misalin yankin dare mai cike da duhu to ku rungumi kur'ani lallai shi mai ceto ne mai cetarwa, duk wanda ya sanya kur'ani jagoransa zai jagorance shi zuwa aljanna, duk wanda yayi wurgi da shi a bayansa zai kora shi zuwa wuta, shi dalili ne da yake shiryarwa ya zuwa mafi alherin tafarki, shi littafi da yake da kunshe da bayani filla-filla da bayani, shi faifaicewa ba kuma wargi ne ba, yana zahiri da badini, zahirinsa hukunci badininsa ilimi.

Lallai wadannan kalmomi da suka gangaro daga gidan wahayi  da risala taskoki ne daga ilimi da ma'arifofin sanin ubangiji, kuma lallai sun cancanci a tsaya a zurafafa tadabburi cikinsu ayi bahasi mai zurfi  da dandakewa, kamar yanda malamanmu suka bugi kirji suka sadaukar da rayuwarsu cikin haka Allah ya jikan wanda suka riga mu gidan gaskiya daga cikinsu ya kuma kare mana wadanda suka wanzu.

Maganarmu ta karshe dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubagijin talikai.  

([1]).الوسائل: باب 21 من أبواب قراءة القرآن الحديث الخامس.

 


Tura tambaya