lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 7 GA RABIU AWWAL SHEKARA 1441, KAN MUSTAHABBANCIN BAYYANARWA CIKIN AZUHUR DA LA’ASAR

Bahasi kan mustahabbancin bayyana karatun bismillar Fatiha da Sura cikin sallolin Azuhur da La’asar

Wuri: Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalu Amil Islami tareda-Assayid Adil-Alawi (H)

Lokaci: karfe 8 na safiya bahasin Fikhu, karfe 9 bahasin Usul

 

Mas’ala 20: mustahabbi ne bayyanar da bismilla cikin sallolin Azuhur da la’asar.

Ina cewa:mene ne hukuncin bayyana bismilla cikin sallolin Zuhraini Azahar da La’asar shin bayyanarwa wajibi ce ko kuma mustahabbi ne ko kuma akwai bayani filla-filla tsakanin limami ya zama wajibi da kuma mai sallah shi kadai ya zama mustahabbi mudlakan cikin raka’o’in biyun farko?

Manyan Malamai sun yi sabani cikin wannan mas’ala, mashhur wanda cikinsu akwai Akaramakallahu Alhilli sun tafi kan mustahabbancin bayyanar da karatun bismilla cikin Azuhur da La’asar babu banbanci cikin kasantuwar ta bismillar Fatiha ce ko kuma ta Sura, ya zo cikin littafin Shaik Dusi Akilaf juz 1 sh 33 da’awar ijma’i kansa, a cikin littafin Almu’utabar: ya sanya hakan daga abubuwa da malamai suka dayantu da su, a cikin Attazkiratu: ya danganta shi ya zuwa ga malamanmu.

Shaik Saduk cikin littafin Alfakihu juz 1 sh 202 da Alkadi Ibn Barraj a cikin Almuhazzab juz 1 sh 92 da wasu daga malamai magabata duk sun tafi kan wajabcin bayyanarwa mudlakan hatta cikin raka’o’in biyun karshe, Abu Salahu Alhalabi cikin Alkafi fil Fikhu: sh 117 ya kebance wajabcin bayyanar da karatun bismilla a iya raka’o’in biyun farko, an samu daga Ibn Junaidu na farko shima ya tafi kan kebantar da mustahabanci a iya kan limami banda mai sallah shi kadai, Muhakkikul Hilli ya kebantar da hukuncin cikin raka’o’in biyun farko.

Ba boye yake ba cewa tushen wannan sassabawa da sabani galibi ya bubbugon daga harshen da riwayoyin suka zo da shi da abin da yake bayyanuwa a zahiri daga garesu musammam ma tareda karo da junansu.

Sai mashhur suka kafa dalili kan mustahabbancin bayyana bismillar Fatiha da Sura a iya raka’o’in biyun farko, kari da haka akwai Ijma’ul mankul da muhassal a kan mas’alar kamar yanda ya zo cikin littafin Almu’utabar da Attazkiratu da Alkilaf cikin jumlar riwayoyi da suka zo cikin babin daga cikinsu akwai: Sahihatu Safwanu:

 (صليت خلف أبي عبد الله عليه السلام أياماً، فكان إذا كانت صلاة لا يجهر فيها جهر بـ (بسم الله الرحمن الرحيم) وكان يجهر في السورتين جميعاً([1]).

Na yi sallah a tsahon wasu kwanaki a bayan Abu Abdullahi amincin Allah ya tabbata a gareshi, ya kasance idan sallar ba a bayyanar da karatun bismilla cikinta ya kasance yana bayyanarwa cikin surorin biyu baki dayansu.1

Fuskar kafa hujja: a bayyane yake kamar yanda yake a zahiri lallai aikin Imami Ma’asumi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yana daga sunna yana kuma shiryarwa zuwa ga rinjayen aiki mudlakan wanda mafi karancin abin da za a kaddara daga rinjayen shi ne mustahabbanci musammam ma daga aikin Imam (a.s) kamar yanda kebantar da Ambato yana daga abin da yake shiryarwa zuwa ga mustahabbancinsa idan ba haka da ya kasance wajibi da babu bukatar ambaton da ya kasance kamar misalin mai fadin na yi sallah a bayansa amincin Allah ya tabbata a gareshi ya kasance yana ruku’u da sujjada.

Daga cikin riwayoyin akwai hadisin Hafsul Sa’igu:  

 (صليت خلف جعفر عليه السلام بن محمد عليه السلام فجهر بـ (بسم الله الرحمن الرحيم) ([2]).

Na yi sallah a bayan Jafar Ibn Muhammad amincin Allah ya tabbata a gareshi sai ya bayyanar da bismilla.

Daga cikin riwayoyin akwai: riwaya mursala daga Abu Hamzatu:

مرسلة أبي حمزة: قال علي بن الحسين عليه السلام: يا ثاني إنّ الصلاة إذا أقيمت جاء الشيطان إلى قرين الإمام فيقول: هل ذكر ربه؟ فإن قال: نعم، ذهب، وإن قال: لا، ركب على كتفيه فكان إمام القوم حتى ينصرفوا، فقال: جعلت فداك أليس يقرأون القرآن؟ قال عليه السلام: بلى ليس حيث تذهب يا ثمالي، إن هو الجهر بـ (بسم الله الرحمن الرحيم) ([3]).

Aliyu Ibn Husaini amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce: ya Sumali lallai idan an tsayar da sallah Shaidan yana zuwa kusa da wanda yake kusa da limami sai ya ce: shin ya ambaci ubangijinsa? Idan ya ce: eh na’am, sai ya tafi, idan ya ce a’a, sai ya hau kan kafadunsa sai ya zama shi ne limami shi yake jan mutane sallah har sai mutane sun idar da sallah, sai ya ce: raina fansarka ba Kur’ani suke karantawa bane? Imam (a.s) ya ce: eh Kur’ani suke karantawa sai dai ba yanda kake tsammani ba ya Sumali, lallai al’amarin yana tareda bayyanar da bismilla.3

ومنها: خبر الفضل بن شاذان عن الإمام الرضا عليه السلام في كتابه إلى المأمون قال عليه السلام: والإجهار بـ (بسم الله الرحمن الرحيم) في جميع الصلوات سّنة) ([4]).

Daga ciki akwai riwayar Fadalu Ibn Shazan daga Imam Rida amincin Allah ya kara tabbata a gareshi cikin wasikarsa zuwa ga Mamun ya ce: bayyanar da bismilla cikin dukkanin salloli sunna ne

Daga cikin akwai abin da ya zo daga jumlar nassoshi daga daga adadin alamomin Mumini kamar yanda Imam Hassan Askari (a.s) daga alamomin Mumini guda biyar.

Daga cikinsu akwai bayyanar da bismilla.

Amma wanda ya tafi kan wajabci ya kafa hujja ne da riwayoyi guda biyu, daya cikinsu itace riwayar da ta zo cikin Alkafi da isnadinsa daga Sulaimu Ibn Kaisu daga Sarkin Muminai (a.s) cikin wata huduba mai tsayi da Imam (a.s) yake cewa:

 (... وألزمت الناس الجهر بسم الله الرحمن الرحيم...)([6]).

An lazimtawa mutane bayyana karatun bismilla.

Ta biyu: riwayar da Saduk ya rawaito daga cikin littafin Alkisalu da isnadinsa daga A’amash daga Jafar Ibn Muhammad (a.s) ya ce

قال: والإجهار ببسم الله الرحمن الرحيم في الصلاة واجب([7]).

Bayyanar da bismilla wajibi ne cikin sallah.

Babban malaminmu Assayid Hakim cikin Mustamsak Alal Urwati juz 6 sh 205 daga Abu Salahi ya tafi kan wajabci a farkon Fatiha da Farkon Sura cikin raka’o’in biyum farko, ta yiwu a hakaito wajabci hatta kan raka’o’in biyun karshe daga Alkazi Ibn Barraj cikin Almuhazzab da Saduk, kamar daga hadisin A’amash daga Jafar (a.s) da hadisin Sulaimu Ibn Kaisu daga Sarkin Muminai (a.s).

Da farko cikinsu: su wadannan riwayoyi a kankin kansu raunana ne ma’ana suna da rauni cikin isnadi, na biyu: kauracewa da mashhur daga malamai sukai daga garesu yana hana jingina da dogaro da su, na uku: akwai ishkali cikin matanin ta farko sakamakon rashin karkatar ta ga sallah, sai a lura.

Hakika Assayid Ku’i yayi munakasharsu cikin Sharhin Urwatul Wuska juz 14 sh 385.

Da farko: hakika abin da ya zo cikin riwayar A’amash yana nan a mahallinsa sai dai cewa bai tabbatu cikin riwayar Sulaimu Ibn Kaisu ba, lallai shi duk da cewa ba a wassaka shi cikin litattafan Rijal ba a bayyane amma dai za a iya sikantar da shi ta fuska biyu: ta farko: daga maganar Ibn Kalid Albarki inda yake cewa: lallai Sulaimu ya kasance daga waliyyan Sahabban Ali (a.s)  littafin Rijalul Barki: 4, daga wannan bayani ya bayyana cewa shi yana daga kebantattun Sahabban Imam Ali (a.s) misalin Komaili daga babban aji da ya wadatu daga wassakawa kamar yanda ake cewa ai wane baya bukatar sai anyi bayani ko shi wane ne sakamakon shahararsa da ilimi da aikin kirki nagari alal misali.

Na biyu: daga bayanin Shaik Dusi cikin Rijal dinsa, Rijalul Dusi: sh 114 ya ce: hakika ya abokanci Ali (a.s) , bayyane yake daga ambatarsa cikin sahabbansa lallai ya zauna da shi, wannan siffantawa bata kebantu da Sulaimu face sakamakon kulawa ta musammam  sai ya zama cewa ya fifitu daga waninsa da kuma kasancewarsa daga kebantattun sahabbansa kuma ya kasance daga waliyyai kamar yanda Ibn Kalidul Barki ya fada, ya kasance cikin abokantakarsa da Imam (a.s) kamar misalin Kumailu Annaka’i Allah ya kara masa yarda lokacin da yake tambayar Imam (a.s) sai ya ce masa: ashe ba kai ne abokin sirrina ba, kamar yanda yanda ya zo cikin addu’ar Kidir ind aya koyar da shi ya ce sakamakon kusancinka da mu da kai kawonka wurinmu sai addu’ar ta shahara da sunan Komaili du’a’u Komailu.

Sannan Assayid Ku’i (K) ya ce: munakashar isnadi cikin wannan riwaya ba cikakkiya bace, bari dai zahirin magana shi ne riwayar ta inganta kamar yanda Allama Yusuful Bahrani ya siffanta ta cikin littafin Alhada’ik juz 8 sh 168.

Sai dai cewa cikin Hamish ya ce: cikin maganar Muhakkikul Hilli (K) akwai munakashar isnadi da wannan ne ya zama riwayar ba cika ba, sannan ya ce: bari dai cikakkiya ce bisa nasarar ra’ayin Assayidul Hakim (K) saboda wanda ya rawaito daga Sulaimu shi ne Ibrahim Ibn Usman wanda ya kasance daga Sahabban Imam Sadik (a.s) da Kazim (a.s) kuma cikin riwayar Sulaimu wanda ya kasance daga Sahabban Imam Ali (a.s)  akwai ishkali sakamakon sassabawar dabakoki kowacce dabaka guda akwai ratar shekaru talati kamar yanda yake a wurin Assayid Burujurdi  (k) kamar yanda ya bayyana cikin ishkalin Assayid Ku’i (K) cikin littafin Mu’ujamul Arrijal juz 1 sh 233/208 ka lura sosai abin da aka ambata daga fuska ta biyu cikin wassakawa ba komai bane face istihsani zanni sannan Assayid Ku’i yayi munakashar riwayoyin ta fuskanin abin da mataninsu yake shiryarwa zuwa gareshi.

Zamu cigaba da yardar Allah ta’ala.

([1]).الوسائل: باب 21 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأول.

([2]).الوسائل: باب 21 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثامن.

([3]).الوسائل: باب 21 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الرابع.

([4]).الوسائل: باب 21 من ابواب القراءة في الصلاة الحديث السادس.

([5]).الوسائل: باب 56 من أبواب المزار .

([6]).الوسائل: باب 38 من أبواب الوضوء الحديث الثالث والكافي: 8: 58/ 21.

([7]).الوسائل: باب 21 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الخامس والخصال: 604 / 9.

 

Tura tambaya