lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

WANI TSONI DAGA HASKE DAGA RAYUWAR AYATULLAHI MUKADDISUL ARDABILI (KS)

 

An nakalto wata kissa da take bayyana kyawuntar dabi’a da badinin babban Marja’in shi’a a zamaninsa a’amarin da yake sanya mutum ya tsaye ya mamaki; yayinda aka nakalto cewa wata rana yana yawo cikin filin ginin Kabarin Imam Sarkin muminai Ali (as) sai wani mai ziyara ya tambaye shi a ina ne zai wanke kayansa ? yayi masa wannan tambaya ba tareda ya san wanne mutum yake tambaya ba, sai Mukaddisul Ardabili yace masa bani ni in wanke maka da kaina!

Wannan wani abun buga misali ne kan duk wani da zai kawo uzuri kan kauracewa hidimtawa muminai maziyarta, wannan wani al’amari ne da yake bayyanar da hakika mai kayatarwa tsarkakka ga wannan bawan Allah wanda samun irinsa ya karanta a wannan zamani.

Bayan yaje ya wanke sai ya dawo wajen wannan Maziyarci ya mika masa kayan a wanke, daidai lokacin da yake hannanta kayan gareshi sai daya daga cikin wanda suka san koshi wanene ya gansu, sai ya zo ya tambayi wannan Maziyarci shin ka san ko wanene wannan da ya wanke maka kayanka? Wannan babban Marja’in shi’a ne, sai wannan Maziyarci ya kama neman uzuri , sai Ayatullahi Almukaddisul Ardabili ya bashi amsa da cewa: ai kai ne kai mini falala kai kake da abin gori kaina saboda kai fa Maziyarcin Sarkin muminai ne amincin Allah ya kara tabbata a gareshi.

An nakalto cewa Sahibuz Zaman (af) ya saka masa da yin maraba da shi duk sanda yayi niyyar ziyara ta yanda kofofin haramin suna budewa gabansa ba tareda an sa makulli an bude su, me yafi girmama daga haka daga tsarkaka da falala! Sai ku lura yak u ma’abota

Tura tambaya