lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Malamai magada Annabawa: tarihin Ayatullahi Assayid Abu Hassan Musawi Isfahani

Shine Assayid Abu Hassan Muhammad bn Assayid Abdul-Hamid Musawi Isfahani, an haife shi a shekaa ta 1284 a daya daga cikin Alkaryoyin da suke karkashin birnin Falarujan da yake karkashin Jihar Isfahan kasar Iran, yana danganewa ga dangi masu riko da addini, haka zalika nasabarsa tare da tsani na karkarewa da mutum talatin da biyu ya zuwa Imam Musa bn Jafar Alkazim (as) ya fara karatunsa a Isfahan a wurin wasu ba’arin malaman addini a can misalin Mahadi Nahawi, da Muhammad Bakir Darja’I da Akun Kashiyu, sannan ya fara karatun nade marhalolin farko-farko daga bahasul kariji A hannun Ayatullahi Jihar Suki da Ayatullahi Abu Ma’ali  da Ayatullahi Muhammad Bakir Darja’i  da Hakim Jahangiri Khan da Akun Kashiyu.

 

A shekara ta 1307hijri ya yi hijira zuwa birnin Najaful Ashraf ya yi karatu a can hannun malaman addini da Maraji’ai misalin Habibnullahi Rasht da Muhammad Kazim Kurasani da Muhammad Kazim Tabataba’i Yazdi _ mawallafin littafin Urwatul Wuska, ya karbi ragamar Marja’iyya bayan wafatin Allama Muhammad Husaini Na’ini sai ya zamanto daga daga manya-manyan maraji’an shi’a da jagororin na addini da siyasa a duniya, Ayatullahi Assayid Abu Hassan Musawi Isfahani ya kalubalanci nada Sarki Faisal na farko a matsayin Sarki a kasar Iraki.

 

Daga cikin siffofinsa akwai saukin kai da kaifin basira da soyayya zuraffafa ga abokai, da kuma yin afuwa ya yi da yake da ikon kan daukar mataki, da hakuri ga wand aya munana masa, da himmatuwa kan al’amuran da suka shafi daliban ilimi.   

Daga cikin wallafe-wallafensa akwai Zakiratu fi Sharhi Zakiratul Muta’allimin da harshen farisanci, da Anisul Mukallidin, shima da harshen farisanci, Manasikul Hajji, shima da harshen farisanci, sannan akwai Zakiratul Ibad Liyaumil Ma’ad, Hashiyatu ala Najatul Ibad, Hashiyatu Muntaabul Rasa’il, Hashiyatul Urwatul Wuska, Sharhul Kifayatul Usul, Wasilatul Najati.

Ya bar duniya a 9 ga watan Zul Hijja shekara ta 1356 hijri a garin Kazimaini mai tsarki da yake kasar Iraki a binne shi a farfajiyar Haidari ta Imam Ali (as) da take Najaf

Ashraf.

 

Daga cikin siffofinsa da dabi’unsa_ akwai batun hakurinsa da juriyarsa: an nakalto daga gare shi cewa wata rana ya ga babban dansa an kashe shi ya yi shahada a hannun daya daga cikin Ashararai sai ya zamanto sam ma bai yi Magana ba face fadin (la’ilaha illallahu) sau uku baga koda digon hawaye ya fito daga cikin idanunsa ba.

Daga cikin dabi’insa akwai amfani da kudade cikin yhada soyayya, an rawaito daga gare shi cewa ya aika da wakili domin tabligi a nusantarwa cikin daya daga alkaryoyi arewacin Iraki, ya yin da wannan wakili nasa ya isa wannan alkarya sai ya zamanto shugaban kabilar garin yaki karbarsa ya hana shi yin tabligi har ta kai ga wakilin ya rasa mafita sai zuwa ofishin `yan sanda na wannan gari domin warware matsalar, sai shugaban `yan sandan ya ce: hanya day arak ta warware wannan matsala shine ka koma Najaf Ashraf ka gaya Assayid Abu Hassan da ya bugawa ministan cikin gidawaya domin ya bamu izinin da kansa domin tsayawa gaban wannan shugaban kabila, sai wannan wakili ya dawo Najaf Ashraf ya gayawa Assayid Abu Hassan Isfahani abin da ya faru sai Assayid ya ce masa, babu matsala zan rubuta wasika ya zuwa shugaban wannan kabila tare da dinare 500, sai wakilin ya karbi wasikar da wannan kudade ya tafi wajen shugaban kabilar, ya yin ya mika masa ya karba sai ya bude yaga wadannan kudade sai ya yi murna ya mika hannun ya gaisa da wakilin ya maraba da shi matukar maraba, ya umarci mutanensa da su hallara majalisinsa da yin sallah a bayansa, tun bayan faruwar wannan lamari sai kabila da shugabanta suka zama magoya bayan Assayid kuma masoyansa, bayan wani lokaci wannan wakili ya dawo birnin Najaf Ashraf ya gayawa Assayid natijojin da aka samu sakamakon wannan wasika da kuma bin wannan hanya da dabara wacce ta fi bugawa ministan harkokin gida waya domin warware matsala, tama yiwu buga masa wayar ya janyo wasu matsalolin sababbi  wadanda bamu bukatarsu.

 

Tsayawarsa kan kare mutuncin wasu: lokacin da ya kasance yana bada wakilcin shari’a ga daya daga cikin wasu mutane sai kuma daga baya ta bayyana cewa wannan mutumi da ya baiwa wakilci bai da cancanta ga wannan matsayi kai tsaye baya janye wannan wakilci ya kasance yana bada amsa ga masu kalubalanta yana mai cewa: gabani bashi wakilcina wannan mutumi ya kasance yanada mutunci a idon mutane, ya yin da dana bashi mutuncinsa da matsayinsa ya karu a idonsu, sai dai cewa kuma ya yinda zan janye wakilcina daga hannunsa zai zamanto ya rasa baki dayan matsayinsa da mutuncinsa, ni gaskiya ban shirya yin tarayya da bada gudummawa ciki zubar da ruwan fuskar kowa ba a tsakankanin mutane.

An rawaito cewa Ayatullahi Uzma Assayid Abdullahi Shirazi Allah ya jikansa cewa: wani matashi dalibi daga cikin daliban addini a Najaf Ashraf ya zo wurin babban Marja’I Assayid Abu Hassan Musawi Isfahani (ks) ya nemi taimako daga gare shi domin yin aure, sai ya ce masa yaje ya zo gobe, bayan gari ya waye sai kwatsam kisan babban dansa ya faru ta yanda makiya sukai masa yankan Rago lokacin d ayake sallah bayan mahaifinsa, lokacin da Assayid Abu Hassan ya halarci raka jana’izar dansa sai cikin wadanda suka halarta yana dinga waiwaye hagu da dama kai kace yana neman wani mutumi ya yin da kallon Assayid ya yi yaw ahar mutane suka fara zaton cewa ko Assayid ya fita daga cikin hayyacinsa ne sakamakon wannan musiba mai radadi data faru sai kawai ya hango wannan matashi ai ya yi ishara gare shi mutane suka kaure da mamakin wannan matashi da yake ishara zuwa gare shi, bayan ya matso kusa sai ya bashi wani dan kulli wanda cikinsa akwai kerarriya zinare 40 sai kowa ya yi mamaki ta yaya Assayid ya kasa manta alkawarinsa na mutumtaka tare da faruwar wannan babbar musiba mai radadi

 

 

Tura tambaya