lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addu’o’i da wuridai masu tarin yawa tareda ba’arin tasirinsu na duniya da lahira

Tareda Alkalamin Samahatus Sayyid Adil-Alawi

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Zan kawo muku wasu ba’arorin samfuri da misali tareda ba’arin tasirinsu na duniya da lahira: duk wanda ya rubuta ayatul kursiyu da ruwan zamzam da za’afaran kan hannun damansa sannan ya sanya harshensa ya lashes hi ya maimaita aikata haka har sau bakwai, lallai haddarsa zata kara karfi

2- domin samun Karin arziki: duk wanda ya karanta

إنَّ اللّه‏ هُوَ الرَّزَّاقُ ذُو القُوَّةِ المَـتِينُ

Tsawon kwanaki 40 kowacce rana sau 20 arzikinsa zai karu.

3- domin Karin arziki: a karanta

 

« وَمَنْ يَتَّقِ اللّه‏ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجا * وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَـيْثُ لا يَحْتَسِبُ »

Har tsawon kwanaki 40 kowacce rana sau 150, idan ya isa ranar karshe sai ya karanta sau 170.

 

4- domin neman samun damar biyan bashi: bayan kowacce sallar farilla a wani fadin kuma bayan sallar asubahi ya karanta

( اللهمّ اغنني بحلالك عن حرامك ، وبفضلك عمّن سواك )

 Sau 110.

5- har ila yau domin sauke bashi: bayan kowacce sallar asubahi ka karanta:

( توكّلت على الحيّ الذي لا يموت ، والحمد للّه‏ الذي لم يتّخذ صاحبةً ولا ولدا ولم يكن له شريكٌ في الملك ولم يكن له وليٌّ من الذلّ وكبّره تكبيرا ، اللهمّ إنّي أعوذ بك من البؤس والفقر ومن غلبة الدين والسقم ، وأسألك أن تعينني على أداء حقّك إليك وإلى الناس ) . وفي آخر : ( ومن غلبة الدين والسقم ، فصلّ على محمّد وآله ، وأعنّي على أداء حقّك إليك وإلى الناس

 

6- domin sauke bashi da cimma muhimman abubuwa: cikin kowacce rana ka karanta  

حقّ ( اللهمّ صلّ على فاطمة وأبيها وبعلها وبنيها بعدد ما أحاط به علمك وأحصاه كتابك )

Sau 70.

7- domin cimma muhimman abubuwa: a karanta (ya Ladifu) sau 120.

 

8- domin neman sauke sarki da cire shi: a samu mutane goma su taru kowannensu ya karanta ayatul kursiyu kafa 10 lallai hakan yana da amfani matuka musammam tara da maimaitawa.

 

9- domin neman Karin hasken idanu: kowacce rana a karanta suratul kadri kafa 21.

 

10- domin sairi na ma’anawiyya cikin duniyar mafarki karanta suartu nuru kafa 66 sau 10

 

11- cikin ayar  

« حَسْبِي اللّه‏ لا إلَهَ إلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ العَرْشِ العَظِيمِ »

Akwai hususiya bakwai: daukaka, izza, yalwa, kwarjini, soyayya, karfi, kudura.

 

12- domin neman biyan bukata wannan ya daga jarrababben hatimin (ya Ali) ayi har tsawon darare 10 cikin kowanne dare a kebantaccen lokaci yayi sallah raka’a biyu sannan ya fuskanci alkibla ba tareda yayi Magana da wani ba yayi salati kafa 110 sannan ba tareda yankewa ba sai yace: (ya Ali) kafa 1570, sannan ya nemi biyan bukatarsa, sai kuma yayi salati ga annabi da iyalansa sau uku, lallai zai samu biyan bukatarsa.

 

13- zikirin (ya Hayyu) bayan kowacce cikin yayi sujjada ya ambaci ya hayyu sau 18 hakan yana tawaita rayuwa da samun aminci daga mutuwar bagatatan ba zato ba tsammani, zai kuma samu yalwa cikin rayuwarsa.

 

14- ya rubuta kuma ya karanta

 

« قُلْ إنَّ الفَضْلَ بِيَدِ اللّه‏ِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللّه‏ُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ * يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِهِ مَنْ يَشَاءُ »

Har zuwa karshen wannan aya mai albarka, lallai tana amfanarwa cikin biyan bukata.

Tura tambaya