lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)

Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)

Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai tsira da aminci su tabbata ga mafificin halittunsa muhammadu da iyalansa zababbu tsarkaka, tsinuwa madawammiya ta tabbata ga makiyansu baki dayansu har zuwa ranar tashin kiyama.

 Daga cikin abinda makarantar ahlul baiti (as) ta fifita da shi shine cudanya tsakanin hankali da nakali da baiwa hankali hakkinsa cikin hukunce-hukuncen shari’ar muslunci, da kuma bayanin gudumawarsa da rawar da yake takawa cikin matafiyar dan adam ya zuwa cikar kamala. Cikin muhimman ingantattunn sakona da kalmomi masu tattarowa cikin bayaninn kimar hankali da daurorinsa da sauran yanayinsa shine shahararriyar wasiyyar majibancinmu imam kazim (as) ga fitaccen almajirinsa hisham ibn hakam (rd)

Da sannu zamu tsakuro abubuwa uku daga cikinta da suke bayani kan muhimman batutuwa.

Batu na farko shine hujjantakar hankali: lallai Allah yanada hujjoji biyu kan mutane: hujja ta zahiri da hujja ta badini, amma hujjar zahiri itace manzon Allah (s.a.w) da sauran annabawa da imamai (as) amma hujjar badini itace hankula.

Ta yiwu ya yi gaggawar bayyana cikin kwakwalwa cewa shi lamarin da’awa ce zuwa hankali da hankaltuwa, wani lokacin kuma zuwa ga annabawa da wahayi, tambaya shine mai dangantaka tsakanin hankali da wahayi?

Shin biyun kishiyoyin junane ko kuma abune guda daya da yake da sasanni biyu da fuska guda biyu babu karo da juna tsakaninsu kamar misalin fuska biyu ga kwabo guda daya.

Lallai kai kace imam (as) daga babin tunkude abin kaddararre lamari ya yi ishara zuwa ga wannan hakika bayyananna wacce duk wanda ya santa sabbin sasanni za su bude gabansa cikin sani da kashafin abubuwa da sirrika ta hanyar mahanagar irfani.

Hakika shine cewa: lallai Allah matsarkaki yanada da hujjoji biyu hujjar zahiri da hujjar badini.

Gabanin kutsawa cikin wannan maudu’i da bayanin abinda ya gasgatu cikinsa da maudu’insu babu laifi idan mu kayi ishara zuwa ga ma’anar hujja da abinda take nufi a luggance da isdilahi:

ance: hujja itace abinda za a iya kafa hujja da shi, ko kuma a kirata da abinda ya ke zuwa bayan Kalmar (saboda shi, ita) ko kuma haddul ausadu da akbar cikin mukadimma biyu sugra da kubra cikin kiyasin da ya fito daga shakalai hudu kamar yadda yake a ilimin mandiki.

Idan mai Magana yace: duniya fararriya ce, sai a ce masa: meye dalilinka da hujjarka kan hakan ? sai yace: saboda ita duniya mai sassauyawa ce sakamakon sauyin dake tareda ita cikin fasalulluka da dare da rana dai dai abinda ya yi kama da haka, wannan shine abinda muke gani a zahiri cikin duniya, saboda haka duniya tana sassauya da canjawa sannan dukkanin mai sauyawa to fararrrene, saboda kuma lallai shi farrare shine abinda wani abu ya gabace shi ko rashin samuwarsa ta gabaci samuwarsa.

Sannan duk mai sauyawa fararre ne, abinda muke san tabbatarwa ya tabbata.

Abinda ya a bayan kalmar (saboda shi) mai sauyawa ne, kamar yadda ya kasance haddul wasad wanda ya maimaitu cikin sugra da kubra, wannan shine abinda ake kira da sugra a ilimin mandik.

Zahirin maganar imam (as) lallai abin nufi da hujja shine dalili da kebantacciyar ma’anarsa, sai ya kasance daga nakali sananne daga ma’anarsa ta lugga zuwa kebantacciyar ma’ana. shine dalili dake danganta shi ga Allah, lallai shi ya wajabtawa kansa rahama, daga babin ludufi, shine abinda ke kusanta bawa zuwa ga ubangijinsa ya kuma nisantashi daga sabo, ya sanya shi kan tsarin halitta hujja dalili na badini da ya ajiyeshi cikin halittar dan adam wannan abu ba komai bane da wuce hankali, haka ma ubangiji ya karfafi hankali hujja ta badini da sanyawa ta shari’a da hujja ta zahiri, wanda sune annabawa da manzanni ma’ana wahayi da shari’a da ta zo daga sama. Lallai biyun hujjojin Allah ne matsarkaki daya ta badini daya kuma ta zahiri wanda suke nuni zuwa ga Allah da hukunce hukuncensa da lamarinsa da siffofinsa da sunayensa, dukkanin abinda hankali ya yi hukunci da shi shari’a tsarkakka na hukunci da shi, wahayi na yin hukunci da shi ma’ana annabi ya yi hukunci da shi ko kuma a wasiyyinsa. Lallai biyun hujjojin Allah ne kan halittunsa.

Lallai Allah yanada hujjoji biyu: hujjar zahiri wadda ake iya gani da tabawa da ta badini wadda kae iya saninta ta hanyar gurabenta da abubuwan da suka kebanta da ita, amma ta zahiri sune manzanni wanda sune ma’abota sako na duniya baki daya kamar misalign annabwa ulul azmi nuhu ibrahiom musa isa da cika makin annabawa muhammadu amincin Allah ya tabbata gareshi da iyalansa da annabawa, lallai Allah ya aiko annabwa dubu dar da ishirin domin shiriyar da mutane tun daga adamu uba ga duk wani mutum ya zua cika makin annabawa shugaban mutane muhammadu (s.a.w) amma hujjar badini sune hankula.   

Daga littafin alkafi da isnadinsa: ibn sukaitu ya cewa baban hassan imam hadi (as) me yasa Allah ya aiko musa ibn imrana da sanda sannan hannunsa kuma fari da kuma kayan sihiri (sanda) sannan ya aiko isa da likitanci ya kuma aiko muhammadu (s.a.w) da kalami da huduba?

Sai abu hassan (as) yace; lallai Allah ya yinda ya aiko musa (as) abinda yafi shahara da tashe a tsakankanin mutanen zamaninsa shine sihiri sai ya zo musu da abinda yafi karfin ikonsu da bazsun iya zuwa da misalinsa ba da abinda ya bata sihirinsu da shi ya tabbatar da hujja kansu ta hanyar wannan sihiri.

Lallai ya aiko isa (as) a lokacinda cututtuka masu cin lokaci da daukar lokaci ba a warke daga garesu suka bayyana kamar misalin shanyewar barin jiki, mutane sun bukatu zuwa ga likitanci a wannan lokaci sai isa ya zo musu daga waurin Allah da abinda basu da irinsa, da abinda ya raya matacce ya warkar da kuturu da makaho da izinin Allah, ya tabbatar da hujja kansu da shi, Allah ya aiko muhammadu (s.a.w) a lokacinda galibi a da shahara a wannan zamani shine kwarewa a zance da huduba ,-ina zaton yace harda wake, sai annabi ya zo musu wa’azozi da hikimomi wanda ya rusa zantukansu da shi ya kuma tabbata da hujja kansu da shi, sai ibn sukai yace: na rantse da Allah ban taba ganin irinka ko da sau guda, to menen hujja kan bayi a wannan zamani? Ma’na cikin sanion annabi da wasiyinsa daga waninsa- sai imam (as) yace: hankali shine abinda ta hanyarsa zaka iya sanin mai gaskiya ka gasgata shi ka san makaryaci ka karyata shi, yace: sai ibn sukaitu yace: wallahi wannan shine amsa.

Wannan dalilim ne bayyananne kan kasntuwar hankali hujja, cikinsa akwai yar fadakarwa cikin cigaban dan adam cikin tanadinsa da tausasar halaye cikin wannan al’umma har su wadatu da hankulansu daga ganin mu’ujizozi na zahiri, lallai shi Imani da mu’ujiza halyya ce ta mutane gama gari hanyace ta gama gari, amma ma’abota yakini da basira basu gamsuwa face da fadadar kirji da hasken yakini

((أَفَمَنْ شَرَحَ اللَّهُ صَدْرَهُ لِلإِسْلامِ فَهُوَ عَلَى نُورٍ مِنْ رَبِّهِ))

Yanzu wanda Allah ya fadadi kirjinsa da muslunci shi yana kan haske daga ubangijinsa.

Da hankali haske da fadadar kirji ake sanin ma’abocin gaskiya kan Allah, da saninsa da littafin Allah da kiyayewarsa da rikonsa da sunnar manzon Allah (s.a.w) da kiyayeta da yake, hakama mai karya kan Allah da jahilcinsa da littafin Allah har yace dukkanin mutane sunfi shi sani hatta matan da suke zaune a gidajen mazajensu da kuma watsinsa da littafin Allah da sabawarsa ga sunna da rashin kulawa da ita, kamar yadda azzaluman halifofin abbasiyawa da banu umayya suka kasance.

Yazo cikin alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah imam sadik (as) yace: hujjar Allah kan bayinsa shine annabi kuma hujja tsakanin bayin Allah da hankali.

Wannan hujja ta hankali zata karbi kammaluwa da karuwa cikin basirarta da hankaltuwarta.  

Daga alkafi da isnadinsa daga imam bakir (as) yace: idan mai tsayuwarmu ya tsaya zai sanya hannunsa a kan kawukan bayi sai ya tttaro hankulansu kwakwalensu su kammalu.

Mai tsayuwa da wannan lamari shine ma’abocin zamani Allah ya gagguata bayyanarsa mai daraja, shine hannun saukar rahama shine tsani samuwarta da fairarsa, sannan kawukan bayi shine ruhinsu mai Magana hankulansu kuma sannan hankulansu sune gangar jikinsu, ya ambaceta da kai saboda shine mafi daukakar abu cikin gabban badini da zahiri, sai imam da wannan hannu nasa mai albarka faira mafi tsarkaka ya tattara hankulansu, sai suka tsinkayi zatukansu suka san ruhinsu da kawukansu suka kammalu da ilimi, suka koma zuwa ga mai musu bayani na asali.

Hankali shine dalilin mumini, babu Imani ga wanda bai san imamin zamaninsa ba, bai da wani hakkoki babu wasu wajibai kansa, farin ciki ga wadanda suka san imaminsu masu kamala makusanta, malamai masu aiki masu tsarkin niyya da ma’abota hankali masu ibada salaihai.

Batu na biyu: dalilin hankali taguwar ma’abocin hankali.

(ya hisham kowanne abu yanada mai shiryar da shi, mai shiryar da hankali shine tunani, mai shiryar da tunani shine yin shiru, kowanne abu yana taguwar da yake hawa, taguwar hankali iatce tawali’u, ya ishe ka jahilci hawan abinda aka haneka hawa).

Majibancinmu imam kazim (as) yana nuni ya zuwa ga wannan gabar cikin hadisin ya zuwa abubuwa uku:

Na farko: yana bijira zuwa bayanin hakikanin hankali da alamomin ma’abocinsa da abinda ke nuni kan hankaltuwar mutum da sanya hankalinsa, da fahimtarsa ga rayuwa tareda kafa dalili da hujja ta hanyar kawo mukaddima biyu kubra da sugra sannan ya fitar da natija daga cikinsu bayan kasantuwarsu lafiyayyu da kuma tabbatuwarsu  hankalce da nassance, daga kubra ya kama cemu mu baku asalai ku kuma sai ku nemi rassa, imam (as) ya kawo ka’idar illa da ma’aluli da sababi da musabbabi wanda ita ka’idar tana daga tabbatattun abubuwa, lallai duk watia illa tanada ma’aluli, lallai shi ma’aluli a kankin kansa yana nuni ya zuwa ga illar data smar da shi ta hanyarv burhanul inni. Kamar yadda itama illa na shiryarwa zuwa ga ma’aluli abinda ta samar ta hanyar burhanul lummi kamar yadda tyake cikin ilimin mandik da falsafa, da ka’idar mujiba kulliya (mai tabbatar baki daya) da kubra cikin kaziyyar da tabbatacciyar ka’ida: lallai kowanne abu yanada dalilin da yake sadarwa zuwa gareshi yake kuma nuni ya zuwa shi, kamar yadda karkashi ka’idar dilala wad’iyyada lafaziyya da dabi’iyya da akaliyya wasunsu.

Sannan shi ma'abocin hankali da ma'anrsa mai gamewa da jinsinsa manisanciyana gasgatuwa knsa cewa shi wani abune dag abubuwa , ya zama dole mu nemi wani dalili da zai shiryar da mu zuwa gareshi akn kasantuwar yanada hankali kuma shi ma'abicn hankali ne, wanda wannan dalili ba wani abu bane da wuce zurfafa tunan. Kamar yadda hankali ke kaiwa ga bukatarsa ta hanyar zurfafa tunani, domin kasntuwar masaukar tunani da zurfafa tunani shine hankali domin ai mahaukaci bai da wani tunani, hakama wawa gabo, ma'abocin hankali yana yin tunani, duk wanda ya yi tunani ya ksance shi ma'abocin hankali ne, domin dayan biyun na nuni ya zuwa daya bisa lazimtuwar juna, dalilin ma'abocin hankali shine zurfafa tunani shi tunani shiune wani motsi daga muradin boyayyen ya zuwa ga mabda na sananne taskatacce cikin samuwar ma'abocin hankali da kuma cikin kwakwalwarsa gabani, wadda ya sameta ta hanyar tsanantuwa da gabban ilimi kamar gabbai mariskai biyar na zahiri(ido, kunne , harshe, hanci, jiki) sannan daga wadancan sanannun abubuwa da tsaraituwa tsakaninsu zai gano boyayyen abu da yake muradi, bayaninsa yana cikin ilimin fasafa da mandik sai a koma domin neman Karin bayani.

Sannan zurfafa tunani da ma'anarsa mai gamewa wadda ke game baki dayan abubuwa na zahiri dana badini kamar yadda ke gamewa da zatuka da ayyuaka da siffofi, shi zurfafa tunani abune kuma kowanne yanada dalili, saboda haka dole ne zurfafa tunani ya zamanto shima yanda dalili, dalilinsa shine lazimatr shiru amma fan a hankali, domin yin shiru a wani lokaci kan kasancewa sakamakjon gazawa ko kasawa ko kuma jin tsoro, irin wannan lazimtar shiru abin zargine yana kuma kasancewa daga shirun jahilci bana hanakali ba.

A wani lokacin kuma kan kasancewa daga hikima da tunani to irin wannan shiru abin yabone, mai yafi yawa daga nassoshin addini da na hankali da suka zo kan mbatun shiru da yabonsa, lallai yadda lamarin yake idan magana ta kasnce daga azurfa to lallai shi kuma rahsinta zai kasance daga zinariya, banbanci nawa tsakanin farshin azurafa da zinariya?

Alamar gane mutum mai hankali na cikin shirunsa  da yawn zuraffa tunanisa koda yaushe cikin halittun Allah, ma'abocin hankali yana cimma abinda yake son cimma ta hanyar tunani.

Taguwa wadda ake hawan gadon bayanta ko kuma wadda ke da sauri cikin tafiyarta. Taguwar da ma'abocin hankali ke hawa shine atwali'u da Kankan da kai da mika wauya zuwa ga umarnin Allah kamewa daga abubuwa da Allah ya hana. Da tawali'u ma'aboicn hankali ke karfafa ya zuwa abinda ke shiryarwa gareshi, zai samu karfafa daga Allah ta hanyar amfani da tawali'u, sanna tareda girman kai da rashin biyayya ga Allah hanakali na raunana.

Ba zai aiki da hankalinsa cikin al'amuransa na yau da gobe. Misalinsa zai ksance misalin mai tafiya da kafafunsa wanda ya gaza cimma bukatarsa.

Bai buy aba kamar yadda muka ambata a baya cewa shi shiru kan kasancewa abin zargi cikin da za ace mutum ya yi shiru kan fadin gaskiya, lallai mai kamewa kan fadin gaskiya shi kurman shaidani, wani lokacin kuma kan kasancewa abin yabo shine wanda ke kasancewa cikin bari magana mara amfani da surutai da baida wata fa'ida da amfani duniya da lahira.

Imam kazim (as) yana cewa hisham: ya hisham karancin magana hikimomine masu girma, na horeku da yin shiru, lalllai shi shiru nutsuwa ne mai kyawu. da karancin laifi, da saukaka nauyayar zunubai , ku katange kofar juriya, lallai kofarsa hakuri, lallai Allah mai girma da daukaka yana kin mutum mai kyakyacewa ba tareda wani abun mamaki ba, da mai yawao da zance ba tareda bukata ba, wajibine kan shugaba ya zama isalin mai kiywo bai gafala daga abun da yake kiwo, bai msu girman kai, kuji kunyar Allah cikin sirrikanku kamar yadda kuke jin kunyar mutane cikin bayyanenku, ku sani cewa lallai kalma guda daga hikima kayan mumini da bace, ku jibanci ilimi gabanin dageshi,

Ya hisham ka koya daga ilimi abnda ka jahilta, ka sanarda da jahilici daga abinda ka koyo, ka girmama malami saboda iliminsa, kayui watsi da jayayya da shi, ka kaskantar da jahili saboda jahilicinsa  amma kada ka koreshi ka kusanto da shi ka koya masa karatu.

Hadisi yaz po kan yabon shiru:

Ya hisham: manzon Allah (s.a.w) yace: iidan kuka ga mumini ma'abocin shiru mai yaan shiru to ku kusance shi lallai shi ana kimsa msa hikima, shi mumini yanada karancin magana yanada yawaita aiki, shiko munafuki yanada yawan magana yanada karancin aiki.

A wani wurin kuma daga wannan hadisi mai daraja: (masu magana kashi uku suke: mai riba lafiyayye, mai halaka kansa: amma mai riba shine mai ambaton Allah, amma lafiyyye shine mai lazimtar shiru, amma mai halaka shine wanda ke kutsawa cikin bat, lallai Allah ya haramta aljanna kan dukkanin mai fadin alfasha mai zage zage mara kunya bai damuwa da dukkaninab inda za a fada kansa.

Abu zarr(rd) ya kasance yana cewa: ya kai mai neamn ilimi lallai wannan harshe dakake gani makullin alherine da sharri kayi hatimi kan bakinka kamar yadda kake buga hatimi kan zinariyarka da takardarka.

A wani wuri imam (as) yace: ya hisham tirr da bawa da yake da fuskoki biyu da harshe biyu zai yabi `dan'uwansa idan suka hadu zai kuma ci namansa idan ya faku daga barinsa, idan aka jarrabeshi sai ya tozarta shi, idan aka maisa kyauta ya yi masa hassada. Lallai mafi saurin alheri da yake samar da lada shine kyautatawa, mafi saurin kawao ukuba daga sharri shine zalunci, lallai mafi sharrin bayin Allah shine wanda ake kyamar zama tareda shi saboda alfasharsa, shin face mutane zasu kifu kan hancinsu sakamakon abinda harsunansu suka girba.

Yana daga cikin kyawuntar musluncin mutum barin abinda babu ruwansa.

Na biyu: imam (as) yana ishara zuwa ga ka'ida kulliya wadda take bamu siffar daga siffofin hankali da ma'abotansa hakan cikin fadinsa cewa kowannne abu yanada taguwa da yake hawa don kaiwa ga bukatarsa, ba komai ne abin hawa da taghuwar ma'abocin hakali ba face tawali'u domin Allah matsarkaki, hakika jumla daga nassoshin addini sun gabacemu da suke nuni zuwa yabon tawali'un masu tawali'u.

Allah madaukaki matsarkaki yana cewa:  

 ((يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَنْ يَرْتَدَّ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ)) [5]

Yaku wadanda sukai Imani duk wanda ya yi ridda daga cikinku ga barin addininsa da sannu Allah zai zo da wasu mutane da yake sonsu suke sonsa suma suke sonsa massu kaskantar daki ga muminai masu izza kan kafirai.

Lallai tawali’u ga mumini yanada daga abinda k samarda da ladada daukaka a duniya da lahira, kamar yadda nuna takabburanci tareda ma’abotansa misalign kafirai ibada ne.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: babu matsayi face da tawali’u, babu matsayi ga bakuraishe babu ga balarabe face da tawali’u, lallai shi tawali’u adone ga matsayi, adone ga daraja, yana kuma yada falala, lallai shi alewar ibada, yanda daga mafi girman abinda ke gasgata ibada, Allah matsarkaki ya kiyantar da girman kai kan annabawa ya yardar musu da tawali’u, suka dora kuncinsu kan kasa suka gogga fusakensu cikin turbaya, suka shimfida fuka fukansu ga muminai, duk wana ya yi tawali’u cikin gidan duniya ga `yan’uwansa shi wurin Allah yana daga cikin siddikai yana daga shi’ar aliyu ibn abi dalibi (as) na hakika.

Tawali’u shine ka bawa mutane abinda kake kaunar kaima a baka. Ma’ana ka baiwa mutane daga kanaka abinda kaima kake so sub aka misalinsa, idan ya ga mummuna sai tunkude ta da kyakkyawa, mai danne fushi mai afuwa ga mutane Allah nasan masu ihsani, daga cikin tawali’u ka yarda daga majalisi ba tareda darajarka, kayi sallama  ga duk wanda aka hadu da shi, kayi watsi da jayayya koda kaine mai gaskiya, tawali’u shine jagaban dukkkanin wani, ka fadi gaskiya koda akanka ne.

Duk wanda ya bar sanya kyakykyawan tufafi saboda tawali'u alhalin yanada ikon sawa Allah zai tufatar da shi da adonsa na karamci,fariin ciki ga wanda ya yi tawali'u saboda da Allah matsarkaki ba tareda yana cikin tauyaya ba, ya kasakantar da kansa ba tareda talauci ba, duk wanda yaje wajen mawadaci sai ya kasakntar da kansa gaban wannan mawadaci saboda dukiyarsa lallai ya yi asarar rabanin addininsa , mai yafi kyawu daga  tawali'un mawadata ga matalauta saboda neman abinda ke gurin Allah, daga cikin tawali'u shine mutum ya ksance bai son a yaba masa bisa takawarsa, tawali'u yana karawa ma'abocinsa daukaka. kuyi tawali'u Allah zai daukaka ku.

Imam kazim (as) yana cewa ( ya hisham rubutacce ne cikin injila: farin ciki ga masu tausasawa juna wadancananka sune ababen tausayawa ranarv kiyama, farin ciki ga wadanda zukatansu ke tsarkake wadancananka sune masu takawa ranar kiyama, farin ciki ga masutawali'u ranar kiyama wadancananka zasu hau mimbarorin mulki ranar kiyama)

Na uku: imam (as) yana fadakar da hisham yana magana da shi kai tsaye yana jan kunnensa daga jahilci makashi wanda ke kai mutum ga halaka, yana magana da shi kai tsaye daidai lokacinda yake isar da sako ga waninsa daga babin

(إیّاک أعني وإسمعي يإجارة)

Da kai nake kiji ya makociya) )

 

فقال: (وکفی بک جهلاً أن ترکب ما نهیت عنه)).

Yace: ishe ka jahilci zakkema abinda ka haneka.

Lallai Allah ya haneka da kasancewa cikin mutakabbirai, lallai shi yace: girma riga tace, shine girma tsantsasaboda cancantarsa ga haka. Yace: duk wanda ya yi jayayya dani cikin girmana ya kasance mutakabbiri kan bayina zan kifa fuskarsa a wuta.

Kayiwa masu girman kai bushara da wuta jahimu da azaba mai radadi, girman kai da takabburanci abubuwa da hankali ya yi hani kan aikata su, saboda suna daga cikin abubuwa dake gasgata zalunci, haka anyi hani kansu a shari'ance saboda hadisai mutawatirai da ayoyi, ta kaka zak sanya girma kai ya zam taguwar da kake hawa tsakanin mutnae, lallai wanna yana daga jahilcin jahil, ya isheka jahilci ka hau wannan takabburanci ka maisheshi taguwarka tareda cewa an haneka ga barinsa a shari'ance da hankalce.

Ya kai ma'abocin hankali kada ka zakkewa abinda aka haneka a shari'ance, saboda shagaltar da zuciya da tunanin abubuwa na zahiri yana ajabta kayyadeta da surantata da sura ta zahiri wadda ke shinge ga abubuwan da hankali ke riska, shi kuma shinge ga barin abubuwan hankali shine ainahin jahilci, sai a fadaka da lura.

Allah matsarkaki ya siffanta iblis la'ananne yace:

((قَالَ فَاهْبِطْ مِنْهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَنْ تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَاخْرُجْ إِنَّكَ مِنْ الصَّاغِرِينَ))

Yace ka sauka daga gareta ba kamaceka kai girma kai cikinta ba* fita lallai kai kana daga kaskantattu.

Ya zo cikin hadisi mai daraja: na haneka da yin girman kai, lallai shi ne m,afi girman zunubai, shine mafi radadin aibobi, shine kayan adon iblis, na haneka da girman kai lallai girman kai ya hana ibis yin sujjada ga adamu.

((أَبَى وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنْ الْكَافِرِينَ))

Yaki ya yi girman kai ya kasance daga kafirai.

Ku fadaka da abinda iblis ya aikata ya yinda ya gurbata aikinsa da ya yi shaikaru masu tsayi, iblis ya yi sujjada tsawon shekar dubu shida na irin shaikarun kiyama ya yi matuakr wahala cikin ibada, shi duk yini daya a kiyama daidai yake da shekaru duba daya a nan duniya, sai dukkanin aikin da ya yi ya lalace sakamakon girman kai na kankanin lokaci, wane wanda bayan iblis zai kubuta daga sabon da iblis ya yi?

Ku kiyaye ya bayin Allah ku yi taka tsantsan daga makiyin Allah kada ya shafa muku ciwonsa. Kada ya fisgeku da kiransa, ku kashe wutar da take ruruwa cikin zuciyarku daga wuatr sabon Allah da gabar jahiliya, lallai wancan kabilanci tana kasne cewa cikin musulmi daga yaudarar shaidani da fizgarsa  da hurinsa, ku dogara da sanya Kankan da kawukanku, da wurgi jiji da kai, da cire rigar girman kai ku riki tawali'u makami tsakaninku da makiyinku iblis, ku wa'azant da abinda ya sai al'ummu masu girman kai gabanenku daga azabar Allah da tumbensa da waki'o'I …. Ku nemi tsari da Allah da barbarar girman kai kamar yadda kuke neman cetonsa daga musibun zamani.

Giramn kai shine abinda ke kasancewa cikin badinin mutum, idan kuma ya bayyana cikin gabbansa sai ya koma takabburanci, na haneku da girman kai lallai shi girman kai yana kasancewa cikin mutum lallai kansa akwai bauta, mafi sharrin aibun hankali girman kai,wani abu daga girman kai bai taba shiga cikin zuciyar wani mutum face ya nakasta hankalinsa gwargwadon wanda ya shige shi kadan ko mai yawa, ku yi taka tsantsan daga girman kai lallai shine jagaban dagawa da sabon ubangiji, girman kai shine  mafi munin halayya, duk wanda ya barranta daga girman kai ya tsira da karama, mutum bai gushewa yana girman kai yana halakar da kansa har sai an rubuta sunansa cikin jabberai sai misalinsu abinda ya faru dasu ya faru da shi.

girma dai kadai na ubangijin talikai ne:  

 ((هُوَ اللَّهُ الَّذِي لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْمَلِكُ الْقُدُّوسُ السَّلامُ الْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ الْعَزِيزُ الْجَبَّارُ الْمُتَكَبِّرُ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ * هُوَ اللَّهُ الْخَالِقُ الْبَارِئُ الْمُصَوِّرُ لَهُ الأَسْمَاءُ الْحُسْنَى يُسَبِّحُ لَهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ))

Shine Allah wanda babu abin baitawa da gaskiya face shi sarki matsarkaki amici mai amintarwa mai tsarewa mabuwayi mai tilastawa mai nuna isa tsarki ya tabbata gareshi daga abinda suke na shirka* shine Allah mahalicci makagi mai surantawa yanada sunaye masu kyau abinda ke sammai da kassai nayi masa tasbihi shine mabuwayi mai hikima.

Banbanci bai buya tsakanin girma da izza.

Wani mutum ya cewa imam (as) lallai cikinka akwai girma, sai imam yace masa: a a, shi girma na Allah shi kadai sai dai cewa cikina akwai izza isa, Allah madaukakin sarki yana cewa:

 ((وَلِلَّهِ الْعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِ وَلِلْمُؤْمِنِينَ))

Izza rinjaye na ga Allah da manzonsa da muminai.

manzon Allah (s.a.w) ya cewa abu zarr (ya abu zarr duk wanda ya mutu alhalin cikin zuciyarsa akwai gwargwadon zarra daga girman kai ba zai shaki kamshin aljanna ba face sai ya tuba gabanin mutuwarsa.

Sai abu zarr yace : ya manzon Allah (s.a.w) lallai ni na kaunaci kyawu har sai ta kai ga na yi burin ace bulalata da gaban takalmina kyawawa ne, shin hakan na zama hatsari garine ? sai yace msa : yaya kake jin zuciyarka? Yace : inajinta tana mai sanin gaskiya da nutsuwa zuwa gareshi, sai yace amsa : hakan ba girman kai bane, shi girman kai shine ka bar gaskiya ka tsallaka zuwa ga waninta , ka dinga kallon mutane ba ka gani wani yanada irin fadinka, jininsa ba irin jinika bane.

Yazo cikin wani hadisin daban : lallai Allah kyakykyawa ne yana son kyau : shi ko girman kai shine take gaskiya da wulakanta mutane da kanana, kamar misalin wanda yake kan dutse, bai da sanin cewa suma mutane haka suke kallonsu kankani dan karami  kaskantacce, idan har ya kasance daga tawali’u akwai karbar gaskiya to lallai girman kai zai kasance inkarin gaskiya da jahiltart, ka rungumi gaskiya lallai ita gaskiya zata nesantaka daga girman kai, sannan yace : ina neman gafarar Allah ina tuba zuwa gareshi  lallai shi ba mai girman kai bane, ba jabberi bane, shi mai girman kai shine wanda ke kafewa kan zunubi da son zuciayrsa tai galaba da shi cikinsa, ya fifita duniya  kan lahirarsa.

Allah matsarkaki na cewa :  

((وَلا تَمْشِ فِي الأَرْضِ مَرَحاً إِنَّكَ لَنْ تَخْرِقَ الأَرْضَ وَلَنْ تَبْلُغَ الْجِبَالَ طُولاً] . ((وَعِبَادُ الرَّحْمَنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الأَرْضِ هَوْناً وَإِذَا خَاطَبَهُمْ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلاماً))

Ka da kai tafiya a doron kasa kana mai Gadara lallai kai baka iya keta kasa ba kuma iya kai tsayi dutse.

Bayin Allah wadanda suke tafiya a ban aksa a saukake idan jahili ya yi musu Magana sai suce aminci.

Batu na uku: abubuwa da ke rusa hankali:

Ya hisham duk wanda ya sallada abubuwa uku kan abubuwa uku to kace shi ya taimakawa son zuciyarsa kan rusa hankalinsa; duk wanda ya duhuntar haske ya kiyanta da tawaitar burinsa, ya goge sabbin hikimarsa sakamakon kalamansa marasa ma’ana, ya kasha hasken fadakarsa da sha’awarsa, kamar ya taimaki son ransa cikin rushe hankalinsa, duk wanda ya rusa hankalinsa, duniyarsa da lahirasa ta baci.

Imam (as) cikin wannan yankin hadisi yana shiga sasannin dan adam  don fassara mana wabni sirrin daga sirrika da wadannan kalami na haske, da wannan dalili na hankali mai zurfin gaske da yake da tsarin tambaya da amsa.

Yana suranta mana hankali da farko kamar matsayin wani karfaffen gini da wata matattakala  madaukakiya , sannan ya suranta mana biyewa son rai mai yawan umarni da mummuna kamar matsayin diga mai rusau ko kuma ace nakiya mai fashewa ami rusawa.

Sannan ya suranta mana wasu digogi da nakiyoyi guda uku wadanda da mutum zai sallada su kan ginin hankalinsa da sun rusa shi su maisheshi baraguzai da kura da isaka ke dauka.

Imam (as) yace: duk wanda ya sallada abubuwa uku kan abubuwa uku to kamar ya baiwa son ransa gudummawa  kan ruguje hankalinsa , natija bayyane take, lallai duk wanda hankalinsa ya ruguje to rayuwa zata kasance ba tareda wayewa da jin ya kamata zai rayu cikin duhu da’airorin tsiyata talauta da haramtuwa zasu kewaya da shi, zai fadi ya zamanto mafi kaskantar makaskanta , duniyarsa da lahirarsa ta gurbata kansa, ya yi hasarar duniya da lahira wadancananka shine hasara mabayyaniya.

Sai dai cewa akwai wata tambaya da tayi ragowa anan shine wai menene wadannan abubuwa guda uku da sukai galaba da kuma ukun da akai galaba kansu?  imam (as) ya yi ishara zuwa cewa:     1- tunanin tsawaita buri yana rusa tushen gini hakakakke

2- surutai barkatai na rusa sabbin benan hikima.

3- sha’awe-sha’awen zuciya na rusa gida mai haskae abin la’akari.

Wadannan daidaiku a bayansu akwai taskar ilima da ma’arifa , a takaice da muna cewa:

Na farko: hasken tunani da tsawaita buri

Hakika ya gabata cewa alamar ma’abocin hankali da dalilinsa shine zurfafa tunani, farkon abinda Allah ya fara halitta ya tsago daga haskensa shine hankali, hankali shi haske ne daga hasken Allah matsarkaki

 (اللَّهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ)

Allah shine hasken sammai da kasa.

Sannan abinda ya lazimce shi daga zurfafa tunani shima zai kasane daga haske, sannan abinda ke kishiyantarsa zai kasnce duhu, tsawaitar buri daga shaidani yake, lallai shi hsaidan an haliceshi daga wuta sannan ita cikinta akwai duhu, sai tsawaita buri ya zamanto  daga duhu, kamar yadda yake kekasar da zuciya, sannan kekasar zuciya daga rundunar jahilci yake  an halicceshi daga duhhai, duk wanda ya duhuntar da hasken tunaninsa ta hanyar tsawaita burinsa cikin rayuwa, lallai shi ya taimakawa son ransa mai yawan umarni da mummuna cikin rusa hankalinsa, saboda tsawaita buri yana mantar da kai tunawa da lahira yana kuma gafalar da mutum ga barin tunawa da ubangijinsa, sai ya rasa hankalinsa wanda ya kasance hakikanin ( abinda aka bautawa Allah da shi aka samu aljanna da shi) wanda bai da hanakli zai shiga cikin garken dabbobi, saboda zai wayi gari cikin galallu sakamkon wannan tsawaita burin nasa. Allah madaukakin sarki yana cewa:

 ((وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيراً مِنْ الْجِنِّ وَالإِنسِ لَهُمْ قُلُوبٌ لا يَفْقَهُونَ بِهَا لَهُمْ قُلُوبٌ لا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لا يَسْمَعُونَ بِهَا أُوْلَئِكَ كَالأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ أُوْلَئِكَ هُمْ الْغَافِلُونَ))

Jahili shine wanda ya kasance azzalimi ko kuma wanda ya duhutar da haskensa da tsawaitar burinsa, lallai shi da tsawaita buri zai dinga rungumart duniya yana fuskantarta da dadinta, sai ya shagaltu ga barin yin tunani.

Ba buya ba cewa tsawaita buri yana hana yin tunanin al’amuran da suka shafi Allah da abinda ya ta’allaka da lahira saboda rai da zuciya a haliccesu kan tunani cikin abubuwan gaggawa da neamn tarkacen duniya da sabubbanta na duhuba komai bace face wani abu mai saurin gushewa.

Babu shakka cewa duk wanda ya sadaukar da tunaninsa cikin hasken lahira vcikin abubuwa da suka ragu nagargaru maimakon tunainsa cikin duhhai cikin am'amurran duniya  wadda ta bayyana ta haifar masa da tsawaita buri da soyayya ga abubuwa masu gushewa.

Na biyu: sabbin hikimomi da zantuka mara fa'ida:

Lallai shi ma'abocin hikima ma'abocin hankali mai tsawaito shiru  mai yawaita aiki yana nesanta daga bani na iya a rayuwance, lallai shi da hankaltuwarsa zai dinga ajiye abubuwa a mahallinsu, bazai dinga bude baki yana magana ba face gwargwadon bukat, bai bada amsa face sai am tambaye shi, baya shiga abinda babu ruwansa, lallai shi shiru alherine sai dai masu lazimatrsa sun karanta, duk wanda hankalinsa ya kammala kalamansa zasu karanta, lallai yawan magana na daga abu mara alafanu, duk wanda ya fiya surutu kurakuransa zasu yawaita, duk wanda kurakuransa suka yawaita ya wofinta himkamrsa ta bushe daga shafin samuwa, kamar yadda zunubansa zasu yawaita , duk wanda zunubansa suka yawaita, zuciyarsa za ta kekashe, duk wanda zuciaysra ta kekashe yana daga cikin `yan wuta, lallaim ita kekashewar zuciya tana daga zirin wuta, kamar yadda rahama take daga zirin aljanna da ni'ima.

Magana abune mai dadi da dada da yake shagaltar da zuciyar daga barin bangaren badini ya juyar dukkanin fafatikarta zuwa ga zabar kyawawan kalmomi, da motsar da zuciya  da hyanyar ishara nukdodin adabi da dai abinda ya yi kama da hakan, sai goge hikimomin da suke tattare da shi daga cikin zuciya ta hanyar biyewa sha'awe sha'awe, saboda so na makantarwa da kurmantarwa daga risker waninsa.

Lallai son biyewa sha'awe-sh'awe ana makantar da zuciya ya kuma tafi da hasken fadakarta, ta kaka  ko zai tsarkaka da tsaftata ya cigaba.   

Idan mutum ya shagaltu da surutai marasa amfani lallai zai shagaltu da manatar da hikima musammam ma a lokacin da yake surutun .

Lallai lokacin da mutane suke jinsa ya soki burutsu da surutai ba zasu bada muhimmanci ga hikimar da take cikin kalamansa ba.

Saboda matuakr zai shagaltu da shiga shar da ba shanu da surutai marasa ma'ana  to Allah zai goge hikima daga zuciyarsa, ya kashe haskaye daga cikin kirjinsa =, duk wanda halinsa ya zama haka  to lallai shi a hakika ya bata addininsa da duniyarsa, bai cikin wanda hankalinsu ya kammalu darajarsu ta daukaka duniya dalahira kamar yadda bayanin hakan ya gabata.

Na uku: haske fadaka da sha'awe-sha'awen zuciya.

Lallai fadaka da wa'azantuwa wani darasi ne da mutum ke daukar daga abinda ke kewaye da shi da kaziyoyi da abubuwa dake faruwa yau da gobe, ita duniya gidan wa'azantuwa ce, me yafi fadakuwa yawaita me yafi karanci daga amsu fadakantuwa, ita fadaka kamar misalin gad ace da aka shimfida da ke daukar daga wannan bari zuwa wancan bari, lallai fadaka da fadakantuwa suna daga cikin alamomin ma'abocin hankali da ma'abocin hikima, kamar yadda fadaka ta kasance daga rundunar hankali, shi hankali da rundunarsa yana daga hasken Alla, fadaka wani haske ne da mutum ke tafiya cikin tarsashinsa domin ya samu haskaka cikin rayuwarsa, mutum yana dauke da karfin sha'awa da fushi, kowacce daya daga cikinsu tamada yanayi guda uku: takaitawa da wuce gona da iri da kuma tsakatsaki, wanda shine falala da sabbinta biyu takatawa da wuce gona da iri wanda suna daga munanan halaye.

Tsakatsaki matsakaici da kuma adalci cikin sha'awa tana daga munana halaye, duk wanda ya kashe hasken fadaka yam aye gurbinsa da sha'awar zuciya lallai ya rushe hankalinsa, duk wanda ya rusa hankalinsa ya gurbatama kansa addininsa da duniyarsa ya kasance wanda mai gurbata addini da duniya, wanna shine hasara mabayyaniya,

Sannan haddin tsakatsaki falala ne cikin fushi wanda shine jarumta, kuma wuce gona da irin cikinta rashin hankali ne, takaitawa kuma ragwanta- bayanin nakn haka dalla dala sai an komawa littafan akhlak kamar misalin littafin jami'ul sa'adat na malam muhakkik naraki (ks) da littafin mahajjatul baida na malama faizul kashani (ks) saii a nemesu.

Magana atakaice shine: lallai imam (as) cikin maganarsa ya karkata da nuni kan cewa cikin mutum akwai karfi guda biyu dake kishiyantar juna wadanda sune: hanaklida soa rai, kowanne dayansu nada siffofi uku da ke kishiyantar dayar, siffofin hankali : zurfafa tunani hikima da fadaka, siffofin son rai: tsawaita burida rawar kai da susrutai da nutsawa cikin sha'awe-sha'awe, sannan kowacce guda tanada gurbi kamar yadda ambaton haka ya gabata .

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsaira da aminci ya tabbata ga Muhammad da iyalansa zababbu tsarkaka.


[1] - سورة الزمر: 22.

[2] - الوافي 1: 112-113.             

[3] - بحارالأنوار 1: 148.

[4] - بحارالأنوار 1: 154.

[5] - سورة المائدة: 54.

 

Tura tambaya